Taƙaitaccen Tarihin Ladidi Tubless - NewsHausa NewsHausa: Taƙaitaccen Tarihin Ladidi Tubless

Pages

LATEST POSTS

Sunday 1 April 2018

Taƙaitaccen Tarihin Ladidi Tubless

A duk lokacin da aka dauko batun aure, wasu da yawa kan yi wa ‘yan fim gani-gani. To amma a wannan karon magana ta kare, domin jarumar da muka tattauna da ita a wannan makon ta ce rashin sani ne ke sa mutane kyamatar auren ‘yan fim.
Idan mutum ya fahimci lamarin kuwa, zai fi wadanda ke auren wadanda ba ‘yan fim ba jin dadin zaman aure, ko me ya sa? Sammam Masu karatu ko kun san shahararriyar jaurmar wasan kwaikwayon ta taba yunkurin shiga aikin soja kafin ta fara wasa? A karanta firar duka a ji:
Taurarin Nishadi

Muna so mu ji cikakken tarihin rayuwarki
Ni dai sunana Ladidi Abdullahi An fi sani na da suna Tubeeless. An haife ni a Kaduna a wata unguwa da ake kira Sabon Gari Nassarawa, wato dirkania ke nan. Na yi Furamare wato a Nassarawa na kuma je makaratar gaba da Furamare.duk a Kaduna wato, ina gama sakandare aka yi min auren fari sai Allah bai yi zamana da mijin ba, sai muka rabu.

Daga nan sai na ji ina son yin aikin kaki, na je na sayi ‘form’ din aikin soja na ruwa na cika na ba da aka kira mu, na je duk abubuwan da ake yi na yi daga, baya ban sake bin ta kan shi kuma ba saboda oda wasu dalillai.
Yaushe kika fara fim din Hausa, da wane fim kika fara, kuma Me ya jawo ra’ayinki kika shiga?
Wata rana sai Rabi’u Rikadawa ya zo gida ya same ni ya ce min, ki zo mu je ki yi aikin fim, shi da Obina. Na ce musu ku je zan zo,

Amma sai na ki zuwa na neme su. Sai muka hadu da Zainab Abubakar muna hira ta ce min, ki zo mu yi aikin fim mana. Na ce mata zan bi ki. Ta ce, min, duk ran da za ta yi aikin za ta kira ni mu je mu yi tare. Na ce mata ba damuwa. kuma kafin nan, muna Hausa ‘drama’ a makaranta dama. Ran da Alfa ‘care’ zai yi wani fim sai ta ce na zo mu je. Na ce mata to, muka je muka gana, sai shi ya tambaya da ma ina fim ne? Saboda ya ga ba na kuskure. Daga nan sai na muka cigaba da zuwa N TA. Oganmu George ya ce,, na iya ‘drama’ ana ta sani. Daga nan kuma ’yan Kano suka zo Kaduna za su yi wani flm sai aka kira ni. Kafin nan mun yi wani flm wanda Rabi’u Koli ya sa Wada Rikadawa ya kira na yi, sai na ciga da aiki sai aka cigaba da kira na ina yi, shi ne. Sai dai na manta shekarar gaskiya. Nasiru Gwagwazo zai yi wani fim Balarabe da Balarabe dila ya kira ina Abuja ya ce na je Kaduna za mu yi wani fim. Shi ma Nasiru Gwagwazo ya kira ni, na ce musu ina zuwa nako zo muka yi.
Fim din da na fara na Turanci ne, shi ne na Alfa ‘care’.
Yaya kike kallon rayuwar mace a fim ‘industry’ yandu?
Gaskiya tun daga Alfa ‘care’ na zo NTA .rayuwar mace a harka fim gaskiya tana fuskantar kalubale sosai.

Mafi yawan lokaci sai a ce ba za a aure ki ba saboda ’yar fim ce, amma kuma rashin sani ne yake kawo haka. Babu mace mai dadin aure da kuma dadin zama irin ’yar fim. Rayuwar mace a fim ‘industry sai dai na ce kalilan ne saboda za ta yi aure komai girmanka kuma komai tashenta wannan shi ne.
A matsayin ki ta tsohuwar ’yar fim, wace shawara za ki bai wa yara masu tasowa yanzu a harkar?
Shawara ta gare su shi ne su yi karatu, saboda na ga gaba abubuwa za su canje wanda zai kai lokaci da sai kana da karatu za ka yi shi kansa fim din ma. In ba ka da karatu wallahi ka zama ‘sorry’. Ita ce kawai shawarata gare su.
Shin Ko Kina da yara da miji kuwa? In da yaran su nawa ne kuma ta yaya kike hada dawainiyar aikinki da hidimar iyali?
Hmmmm! Ba ni da yara, amma insha Allahu zan yi aure kuma zan haihu, amma yanzu kam ba ni da ko daya.

Ko Kina da sha’awar ‘directing’ ko ‘producing’ fim na kanki nan gaba?
Na yi ‘producing’ har sau 5, amma ban ji dadi ba, a gaskiya, saboda haka na bari na hakura na koma ‘acting’ dina kawai.
A karshe shin bayan fim kina wani sana’ar ne ko Aikin ofis?
Baya ga fim ba na wani aiki .amma ina yin aure zan nemi aiki, saboda mijin da zan aure ba zai bari na yi fim, ba. Zan kakkabe kwalina na nami aikin ofis, tun da ina da kwali kuma don haka ne na yi karatun.
Mun gode sosai da hadin kan da kika ba mu, Allah ya taimaka
Ni ma na gode da kika ba ni lokaci na amsa sa tambayoyin. Na gode Allah ya raya zuriya.
©Leadership



Copy the link below and Share with your Friends:

Download Our Official Android App on Google Playstore HERE
OR
Download from another source HERE



No comments:

Post a Comment