An Bayarda Belin Salman Khan - NewsHausa NewsHausa: An Bayarda Belin Salman Khan

Pages

LATEST POSTS

Saturday 7 April 2018

An Bayarda Belin Salman Khan


Wata kotu a kasar India ta bayar da belin jarumin fina-finan Bollywood Salman Khan, wanda ta yanke wa hukuncin daurin shekara biyar a gidan yari.

 Ranar Alhamis Din Da Ta Gabata ne kotun ta yanke wa jarumin hukuncin bisa samunsa da laifin yin farautar gwankin da ba kasafai ake samunsa ba, ba bisa ka'ida ba.

Kotun, wadda ke zamanta a Jodhpur, ta kuma ci tarar jarumin rupee 10,000 kwatankwacin dala 154.

Salman Khan dai ya kashe wasu nau'in gwanki da ake kira blackbucks guda biyu a yammacin jihar Rajasthan a yayin da ake daukar fim din Hum Saath Saath Hain a shekarar 1998.

Kotun dai ta wanke sauran jaruman da suka fito a fim din tare su hudu.

Tun da fari dai, lauyan jarumin mai shekara 52, ya gabatar wa kotun hanzarin mutumin da yake Wakilta A cewarsa, daurin shekara biyar zai haifar da koma-baya a sana'arsa ta fim.

Rahotanni sun ce dole ne Salman Khan ya zauna a gidan yari na wasu kwanaki.

An Yanke Wa Jarumin Bollywood Salman Khan Hukunci Shekara Biyar A Gidan Yari

Copy the link below and Share with your Friends:

Download Our Official Android App on Google Playstore HERE
OR
Download from another source HERE



No comments:

Post a Comment