Abin da yasa Nafisa Abdullahi ta kama Gida Kaduna
Jaruma Nafisa Abdullahi ta na daya daga cikin jarumai mata a Kannywood da suka dade ana damawa da su.
Jarumar ta yi mana bayanin dalilin da yasa ta kama gida a Kaduna, da kuma wasu abubuwan da su ka shafi rayuwar ta.
Ga yadda hirar ta mu ta kasance.
Ga ki kinga jiya kuma kinga yau kuma har yanzu ba'a daina yayinki ba Masoya na Son fina-finanki minene Sirrin?
Sirrin shine Allah na rike da ni, kasan komai a duniyar nan idan kaga mutum yana yin Sa, Idan bai nufeshi ba da yin sa ba, to ba zai taba yi ba, kuma ko da yanayin Abun idan Allah bai rikeshi ba sai kaga abun ya zama wani iri. Abinda zance kawai Allah ke rike dani.
Ko akwai wani Darasi da kika dauka a shigowarki masana'anatar Fim?
Dole mutum yana da darasin dauka, idan ka shigo masana'antar fim, ko kuma idan zaka shigo, kawai dai mutum ya tabbatar da Abinda ya kawoshi zaiyi, idan Fim din kazo ta ya zamto da gaske Fim din kazo, idan kuma ba Fim kazo yi ba ka shigo masana'antar, ba dai zan tsaya badai zan tsaya ina bayanin yanda Abubuwan suke kasancewa ba.
Wadanne nasarori kika samu daga lokacin da kika shigo Harkar Fim zuwa yanzu?
Na samu nasarori gaskiya da dama, kusan zan Iya cewa babbar nasarar duk da dai kasan wani yana yin Fim din ne saboda abinda ya keso ne, wani lokacin kuma za kayi ne don ka fadakar da mutane, To Alhamdulillahi sakona yana isa ga Jama'a kuma suna amafani dashi, kaga shima wannan babbar nasarace banda abun Duniya da dama wadanda na samu.
To wane kalubale kuma kike fuskanta?
Kalubale dai bai wuce kasan yadda mutane sun saba ganina na fito abun tausai, to idan ya zamto Na sanya kananan kaya matsatstsu to har yanzu akwai wadanda ke daukar Fim kamar dagaske ne, shima wannan Babban kalubale ne, sai daga lokacin da suka daina ganina da abun, suka fahimci Fim suke kallo. To daga nan Babban kalubalen da nake fuskanta zan daina fuskantar sa.
Kwanakin baya a shafinki na Instgram munga kina maidawa masu aikin Jarida Raddi ko akwai wani Abu da ya hadaki dasu?
Ba wani abu ya hadani dasu ba, kasan wani lokacin akwai irin kananan abubuwan da mutum ya kan fada Wanda bai kamata a daukeshi babban abu ba, kamar maganar da akayi wadda tasa har nayi wannan maganar itace nayi magana kan mata masu bleaching mutum ya tsaya yanda Allah yayishi, ba sai yayi wani abu ba kafin namiji ya soshi, to ni na yarda da hakan. Idan ina da saurayin da yake son mace fara ba zance dole sai na zama fara ba kafin ya soni, idan sona yake dagaske zai soni ne yanda Allah ya yoni ba yanda yake so ya ganni ba. Kaga irin wannan maganar ba zaka daukeshi irin babbar matsala bane, kuma wani lokacin akwai abubuwa da dama wadanda suke faruwa da wasu jaruman maza da mata Wanda ya kamata ace an daukesu anyi magana a kansu, Amma wani lokacin ba'ayi. Kuma bance 'Yan jarida na da matsala ba. Amma akwai wadanda basu daukar abun alheri sai sharri suke dauka, Amma ba duka 'Yan jaridan suke haka ba. Dalilin da yasa nayi maganar kenan Amma ba wani Abu bane ya hadani dasu ba.
Wane Buri kikeso ki cimmawa? ganin cewa duk wani abu da ya kamata ace mace ta samu a harkar nan ke ma kin samu.
Eh maganar da ka fada hakan gaskiya ne, to Amma ni a matsayina na 'Yar wasa akwai abubuwan da Na keso Wanda mu a masana'antar mu ta hausa tunanin wasu bai kai ga wajen ba, bayan akwai abubuwan da nake nema wadanda ban samu ba a harkar, akwai aure a raina kaga lokacin da wasu abubuwan za Suzo idan Allah ya taimaka bana nan. Kaga kenan zan Iya cewa ban cika cimma burina ba tunda har yanzu banyi abun da nakeso nayi ba.
Mi kika fi so a rayuwarki Wanda ke sanyaki farin ciki?
Idan kaga ina cikin farin ciki da raina, irin na hadu da kananan yara 'Yan shekara 2 zuwa 3 masu kaunata. Irin wannan abun ba karamin farin ciki yake sanyani ba, ban saniba ko suma sauran suna jin haka don nidai gaskiya inason yara kanana da sauransu.
Mi kuma yafi baki haushi a Rayuwarki?
Gaskiya akwai abubuwa wadanda ke bani haushi wanda ba sai na tsaya ina cewa kaza da kaza ne suke ban haushi ba, nidai banason negative Abu Wanda zai jawomin tsangwama koma minene gaskiya bani sonshi.
Ko akwai wata Sana'a da kikeyi bayan harkar Fim?
Inada Sana'a mana inada shirin bude Shago Na sayarda kayayyakin sawa na suttura, Amma yanzu bai fara aiki ba.
Ance kin Kama gida a kaduna minene gaskiyar Labarin?
To! Ikon Allah! Ya zama batu kenan? To bari na tambayeka zaman hotel ba issue bane? Yanzu idan naje kano, Abuja, Zariya da sauransu a hotel nake zama, Gidan iyayena a jos yake bana aiki a jos kuma idan naje jos din baifi inyi kwana 3 zuwa 4 ba, na Dade da yawa sati guda, kaduna ne kawai nafi zama kuma a wurin nake aiki, idan zaman hotel dina ya zama issue mi ya kamata nayi ba In kama gida ba, kuma Gidan ma wanda ba koda yaushe nake zama ba, domin ina zuwa wurare da dama, ko kuna tunanin duk Inda nake zuwa zan sayi gidane? Ai bazai yiwuba Allah bai kaddaramin wannan matsayin ba tukunna. To idan na kama gida ai ba wani Abu bane ko ni Na fara? Kaga kenan ba abun magana bane. Da kama gida da zaman hotel wanne yafi ai kaga gwara kama gida.
Minene gaskiyar labarin cewa an sanya maki biki Amma ba ki fadi da Wanda aka sanya maku ba, sai lokacin bikin ya matso zaku sanar?
Nan dai ban saniba, bansan ko masu maganar ne suka sanyamin ranar ba, babu wannan maganar gaskiya, Amma inada manema kuma inada Wanda Na keso, Kuma insha Allahu Wanda nakeso din ne zan aura.
Ko Dan Fim ne zaki Aura?
To minene aibun Dan Fim? Mi zai hana Na auri Dan Fim, Ba Dan Fim zan aura ba, inada Wanda zan aura Na fitar dashi Amma ba Dan Fim bane.
Ance bakison ana maki maganar Adamu Zango shin gaskiyane?
To yanzu da kayi min maganar Adamu zangon mi nayi maka? A gayamin wane dalili ne ba zanso a yimin maganar Adamu Zango ba, hasalima idan ana aiki idan ba'a yimin maganar shi ba, ni zanyi wa mutane maganar sa, to wannan zancen mutane ne, mutane ma akwai Su da bata lokacinsu.
Kin taba nadamar shigarki harkar Fim kuwa?
Idan kaga mutum yayi nadamar yin abu, to rashin dadin abun yafi dadinsa yawa, to ni a nawa bangaren dadin ya linka rashin dadin nesa ba kusa ba. Kaga kenan babu yanda zance nayi nadama. Banyi nadamar shigowata hausa Fim ba, Inda ace za'ayi banda duniyar nan da muke ciki, idan aka tashi halittomu kila abun da nakeso nayi kenan harkar Fim. To banyi nadama ba.
Daga karshe wane sako ko Albishir kike dashi ga masoyanki?
Sakona garesu shine suci gaba da kaunta, kamar yanda sukeyi kuma nima ina kaunarsu nagode Allah yabar zumunchi.
Copy the link below and Share with your Friends:
No comments:
Post a Comment