Ganawar Mukaddashin Shugaban Kasa Da Dattawan Arewaci Da Kudanci Na Iya Zama Taron Shan Shayi ? Inji Kungiyar Matasan Arewa - NewsHausa NewsHausa: Ganawar Mukaddashin Shugaban Kasa Da Dattawan Arewaci Da Kudanci Na Iya Zama Taron Shan Shayi ? Inji Kungiyar Matasan Arewa

Pages

LATEST POSTS

Friday 16 June 2017

Ganawar Mukaddashin Shugaban Kasa Da Dattawan Arewaci Da Kudanci Na Iya Zama Taron Shan Shayi ? Inji Kungiyar Matasan Arewa

Ganawar Mukaddashin Shugaban Kasa Da Dattawan Arewaci Da Kudanci, Na Iya Zama Taron Shan Shayi Matukar Ba A Dauki Matakan Da Suka Dace Ba, Inji Kungiyar Matasan Arewa

Daga Ibrahim Ammani Kaduna

An bayyana ganawar da Mukaddashin Shugaban Kasa Yemi Osibanjo yayi da Dattawan kasashen Inyamurai da wasu Dattawa daga yankin Arewa, a matsayin wani mataki da ya dace amma a hannu guda ganawar na iya zama taron shan shayi, muddin ya zamana ba'a dauki matakan da suka dace ba na warware asalin rikicin. 

Bayanin haka ya fito ne daga bakin daya daga cikin Shugabannin gamayyar Kungiyoyin Matasan Arewa 16 wadanda suka bada wa'adin watannin uku ga dukkanin Inyamurai na da su fice daga nahiyar Arewa mai suna Alhaji Nastura Ashir Shariff, lokacin da yake tattaunawa da Manema Labarai a Otel din Quarter House dake Garin Kaduna. 

Alhaji Sharrif ya cigaba da cewar babu wani babba daga yankin Inyamurai wanda ya fito ya soki lamirin abinda tsagerun Inyamurai karkashin jagorancin Nnamdi Kanu suke yi, face yaba musu da kuma mara musu baya da suke yi, saboda haka ganawar su da Mukaddashin Shugaban Kasa zai iya zama aikin Baban Giwa, kasancewar tsofaffin na Kasar Inyamurai na goyon baya Dari bisa Dari ga tsagerun Matasan Inyamuran masu rajin kafa yankin Biafra, saboda haka kamata yayi Shugabannin Kasa suyi zama kuru-kuru da Matasan Inyamuran domin suyi bayani na zaba cikin biyu Nijeriya ko Biafra. 

Dangane da ziyarar da tsohon Dogarin tsohon Shugaban Kasa Marigayi Sani Abacha wato Manjo Hamza Al Mustafa mai ritaya ya kawo kwanakin baya a garin Kaduna, inda ya gana da wasu daga cikin shugabannin Inyamurai, Ashir Shariff ya tabbatar da cewar su a matsayinsu na shugabannin Kungiyoyin Matasan Arewa ba su aiki kowa ya gana da Inyamurai ba, Hakazalika su a matsayinsu na wadanda suka yi wancan magana ta bayar da wa'adin korar Inyamurai babu wanda ya gayyace su wannan taro, wanda hakan ya nuna cewar da akwai akasi kenan, kuma Inyamurai Matasan su da tsofaffin su sun san su waye Matasan Arewa, kuma sun san hanyar da zasu nemi ganawa dasu, amma sai su kayi kwana suka gana da Al Mustafa, wanda hakan ke gwada cewar sun bar Jaki da gangan sun koma dukan taiki kenan. 

Kungiyar Matasan Arewan sun kara da cewar, ko kadan ba su da bukatar cigaba da zama da Inyamurai a tarayyar Nijeriya muddin Inyamuran na cigaba da nuna kyama da wariya ga Jama'ar Arewa, sannan lallai ne Shugaban Kasa ko Mataimakin shi suyi zama a fili da Matasan Inyamurai su furta da bakin su suna bukatar cigaba da zama a Nijeriya ba wai an yi musu dole ba ne, kuma duk wanda suka zaba a ciki Kungiyar Matasan Arewa na marhabin da shi ba tare da wani jinkiri ba. 

Matasan Arewan sun kuma tabbatar da cewar wannan fafutuka da suke yi na neman 'yancin Jama'ar Arewa su nayi ne bakin rai bakin fama, kuma basu shakkar dukkanin wani bara gurbi dake da mukami a Arewa wanda zaiyi barazanar kama su ko kuma wasu tsofaffi da zasu ki mara musu baya, domin ko an ki ko an so dole sune zasu gaji Arewa, wadancan tsofaffi tasu ta riga ta kare, saboda haka ya dace suyi shiru shine alkhari a garesu. Daga karshe Matasan sun bayyana cewar za suyi wani gagarumin taro a ranar Talata mai zuwa a garin Kaduna domin kara fito da matsayinsu akan dukkanin wani Inyamuri ko wani bara gurbi a yankin Arewa.

Sources:Rariya

Copy the link below and Share with your Friends:

Download Our Official Android App on Google Playstore HERE
OR
Download from another source HERE



No comments:

Post a Comment