Akwai yiwuwar Buhari zai dawo Najeriya ranar Asabar - NewsHausa NewsHausa: Akwai yiwuwar Buhari zai dawo Najeriya ranar Asabar

Pages

LATEST POSTS

Tuesday 6 June 2017

Akwai yiwuwar Buhari zai dawo Najeriya ranar Asabar



- Wasu majiyoyi daga fadar shugaban kasa sun bayyana cewa, ana sa ran cewa shugaban kasa Muhammad Buhari zai dawo gida Najeriya a ranar Asabar mai zuwa

- A yau Talata ne uwargidan shugaban kasa ta dawo daga birnin Landan bayan ziyara da ta kai ma mijin nata

- Ta nuna godiya ga ‘yan Najeriya bisa ga addu’oin su ga maigidanta

Wasu majiyoyi daga fadar shugaban kasa sun bayyana cewa, ana sa ran cewa shugaban kasa Muhammad Buhari zai dawo gida Najeriya a ranar Asabar mai zuwa.


NAIJ.com ta tuna cewa a ranar 7 ga watan Mayu ne, shugaba Buhari ya tafi birnin London don duba lafiyarsa bayan ya mika ragamar mulkin kasar a hannun mataimakinsa Farfesa Yemi Osinbajo.

Har ila yau a safiyar yau Talata ne uwargidan shugaban kasa Aisha Buhari ta dawo gida Najeriya bayan ta kai wa maigidan nata ziyara a can inda yake jinya wato birnin Landan.

Ta kuma sanar da cewa shugaba Buhari na samun sauki sosai kuma zai dawo nan bada jimawa ba domin ya daura daga inda ya tsaya.

Daga karshe kuma ta yi godiya ga ‘yan Najeriya bisa tarin addu’oi da kuma fatan alkhairi da suke yi ga maigidan nata

Copy the link below and Share with your Friends:

Download Our Official Android App on Google Playstore HERE
OR
Download from another source HERE



No comments:

Post a Comment