Daga: Ibrahim Baba Suleiman
A ranar alhamis dinnan mai zuwa (16/3/2017 (wato 17/6/1438AH) in sha Allah. Kungiyar Izala zata fara zagaye zuwa wajen 'ya'yanta a jihohi 37 harda Abuja da ke fadin kasar Naijeriya
Shugaban kungiyar ta tarayyar Najeriya Sheikh Abdullahi Bala Lau ya shaidawa manema labarai cewa, kungiyar zata zagaya zuwa jihohin ne domin ganin yadda ayyukan kungiyar suke tafiya a lungu da sako tare da wasu birane na sassan kasar.
Zagayen wanda za'a fara da jihohin Bauchi, Gombe, Adamawa da taraba, Manufar zagayen shine 'Karantar da masu wa'azi' domin inganta harkokin Da'awa zuwa ga wadanda basu fahimci addinin islama ba, tare da farfado da harkokin ilimi a makarantun Islamiyya da dai sauran su.
Jadawalin zagayen na farko zai kasance kamar haka;
Kwana daya aka kebewa kowace jiha.
Jihohin farko sune-
Bauchi 16/3/2017,
Gombe 17/3/2017,
Adamawa 18/3/2017
Taraba 19/3/2017.
Tawagar da zasu raka Shugaba Sheikh Bala Lau ta hada da wasu shugabanni, Malamai da daraktocin kungiyar a matakin kasa, zata sauka a birnin Bauchi da misalin karfe 12 na ranar Alhamis 16/3/2017 in sha Allah.
Sanarwa daga ofishin babban sakataren kungiyar ta kasa, Sheikh Muhammad Kabiru Haruna Gombe.
#Jibwis_Nigeria
13/Jumada Awwal/1438
12/March/2017
Copy the link below and Share with your Friends:
No comments:
Post a Comment