Tambaya:
Assalamu alaikum wa rahmatullahi wa barakaatuhu, Don Allah malam mene hukuncin yin fitsari a tsaye ga mace ko namiji a Musulunci?
Amsa:
Ya halatta ga namiji ya yi fitsari a tsaye, saboda hadisin da Bukhari ya rawaito cewa: "Annabi S.a.w ya je jujin wasu mutane sai ya yı fitsari a tsaye"kamar yadda Bukhari ya rawaito a hadisi na 222...
Tare da cewa duk hukuncin da ya zo dağa Annabi s.a w. yana hada mace da namiji, in ba'a samu abin da ya kebance shi ba, Tabbas fitsarin mace a tsaye zai jawo matsala wajan cikar tsarkinta, saboda yanayin halittar da Allah ya yı mata.
Yana daga cikin Ka'idojin sharia gabatar da wajibi akan abin da aka halatta, yin fitsari a tsaye ya halatta ga mace, saidai zai kai ga kunci wajan tabbatar da Dhahara, wacce sallah ba ta ingantuwa saida ita.
Duk hadisan da suka zo cewa Annabi ya hana yin fitsari a tsaye ba su inganta ba, sai hadisin Nana A'isha wanda HakiM ya inganta, in da take cewa : "Duk wanda ya ce muku Annabi s.a.w ya yi fitsari a tsaye kar ku gaskata shi" kamar yadda Nasa'i ya rawaito a hadisi mai lamba ta: 29.
Malamai suna cewa : za'a dau maganarta akan tana bada labari ne, akan abin da ta gani, wannan ba ya kore a samu wani abin daban wanda ba ta sani ba, tun da ba koyaushe take zama tare da shi ba, yana daga cikin Ka'idoji a wajan malaman Usulul-fiqhi : Duk wanda ya tabbatar da abu za'a gabatar da maganarsa akan wanda ya kore, saboda wanda ya tabbatar yana da Karin ilimi na musamman wanda ya buya ga wanda ya kore.
Don neman Karin bayani duba : Sharhu Assuyudy ala Sunani Annasa'I 1\26.
Allah ne mafi sani.
Dr Jamilu Zarewa
8\3\2016
Copy the link below and Share with your Friends:
No comments:
Post a Comment