Tambaya
Assalamu alaikum, malam INA da wata
tambaya shin menene hukuncin yin bacci
bayan sallar asuba? Allah ya taimaki malam!
Amsa:
Wa alaikum assalam.To malam babu wani hadisi mai inganci wanda ya hana bacci bayan sallar asuba, sai dai bayan sallar asuba lokaci ne mai albarka, wannan yasa Annabi S.A.W idan ya yi sallar asuba baya tashi daga wurin sallar sai rana ta fito, haka ma sahabbansa Allah ya yarda da su, kamar yadda Muslim ya rawaito a hadisi mai lamaba ta: 670.
Kuma Annabi s.a.w yana cewa: "Allah ka sanyawa al'umata albarka a cikin jijjifinta" Tirmizi a hadisi mai lamba ta: 1212, kuma ya kyautata shi.
Wannan yake nuna cewa lokaci ne mai
albarka, wanda bai dace da bacci ba,
wannan ya sa ko da rundunar yaki Annabi
s.a.w. yake so ya aika, yakan aikata ne afarkon yini saboda albarkar lokacin.
Wasu daga cikin magabata, sun karhanta
yin baccin bayan sallar asuba, Urwatu dan Zubair yana cewa : "Idan aka ce min wane yana baccin safe na kan guje shi' kamar yadda Ibnu Abi-shaiba ya ambata a
Musannaf dinsa 5\222.
Ya kamata ka shagala da neman ilimi ko
kosuwanci a irin wannan lokacin.
Allah ne mafi sani.
Amsawa
Dr. JamiluYusuf Zarewa
30/01/2015
Copy the link below and Share with your Friends:
No comments:
Post a Comment