Dan Fodiyo Ya ce :- Yin Maulidi Bidi'a ce Abar Kyamar Ga Hujja kamar Haka Dr Ibrahim Jalo Jalingo - NewsHausa NewsHausa: Dan Fodiyo Ya ce :- Yin Maulidi Bidi'a ce Abar Kyamar Ga Hujja kamar Haka Dr Ibrahim Jalo Jalingo

Pages

LATEST POSTS

Monday 20 November 2017

Dan Fodiyo Ya ce :- Yin Maulidi Bidi'a ce Abar Kyamar Ga Hujja kamar Haka Dr Ibrahim Jalo Jalingo


SHEHU Dan Fodiyo ya ce cikin littafinsa: Ihyaa'us Sunnah Wa Iqmaadul Bid'ah shafi na 104 :-
((فان قلت ما حكم ما يفعل الناس في شهر ربيع الاول في يوم المولد او اليوم السابع من المولد من اجتماع الناس للذكر والطعام الذي يعملونه لذلك؟ قلت: انه بدعة مكروهة ان خلا عن كل معصية. وقيل: ان الصواب ان عمل المولد الشريف النبوي من البدع الحسنة المندوبة اذا خلا عن معصية. وأما ما يعتاده الناس في هذا الزمان في ذلك من اختلاط الرجال والنساء فمعاذ الله ان يقول احد بجوازه)).
Ma'ana: ((Idan ka ce: Mene ne hukuncin abin da mutane suke yi a cikin watan Rabii'ul Awwal a ranar maulidi, ko kuwa a ranar bakwai ga maulidi na taruwar jama'a saboda yin zikiri, da cin abincin da aka yi tanadinsa saboda hakan? Sai in ce: Wannan bidi'ah ce makruuhiyah in yin maulidin ya kubuta daga dukkan sabon Allah. (A wani kaulin kuma) an ce: Abin da yake daidai shi ne: shirya maulidin Annabi yana daga cikin bidi'o'i masu kyau da a ake so matukar dai ya kubuta daga ko wane sabon Allah. To amma abin da mutane suka Saba yin shi a maulidi a wannan zamani na cakuda tsakanin maza da mata A'uuzu Billaahi wani ya yadda da halaccinsa)).

A cikin wannan magana ta Dan Fodiyo rahimahullah za mu fahimci abubuwa kamar haka:-
1. Fatawar Shi Dan Fodiyo ita ce: Bukin Maulidi bidi'ah ce abar kyama.
2. Akwai wata magana da ke cewa: Bukin Maulidi bidi'ah ce abar so, to amma shi Dan Fodiyo yana ganin wannan magana ce mai rauni, shi ne ma ya sa ya hikaito ta da sigar: an ce.

Allah Ka tausaya wa al'ummarmu ka cusa musu kin bidi'ah. Ameen.

Copy the link below and Share with your Friends:

Download Our Official Android App on Google Playstore HERE
OR
Download from another source HERE



No comments:

Post a Comment