Daga Ibrahim Ammani Kaduna
An bayyana munmunan matakin da Maryam Sanda ta dauka na kisan Mijin ta Bilyaminu Bello Halliru da cewar, mataki ne wanda ya nuna a fili cewar ba ta samu ilimi na addinin Islama ba, sannan babban dalili ne da ya tabbatar da cewar ba ta samu kyakkyawar tarbiya daga gida ba.
Shugabar gidauniyar Ummul Khairi Foundation da ke Kaduna Hajiya Maryam Yahaya Sani ta bayyana hakan, lokacin wata ganawa da manema labarai da tayi domin nuna damuwar ta akan bata sunan Musulunci da Matan Arewa da Maryam Sanda ta yi, a Ofishin gidauniyar ta ta dake garin Kaduna.
Shugabar ta Ummul Khairi ta cigaba da cewar, duk inda ka ga Mata masu tsananin bakin kishi da rashin imani irin na Maryam Sanda, to kada ma a yi wata tababa tsagwaron jahilci ne da rashin tarbiya ya kai su ga haka, domin shi addinin Musulunci bai bar komai ba, da Allah ya umarci Maza da auren Mata hudu wata hikima ce daga Allah, kuma dukkanin mai hankali ya gane wannan hikimar, to a bisa ga wannan a samu wata Mace ta fito tace bata yadda Mijin ta ya kara aure ba, babu shakka tayi fito na fito ne da dokokin Ubangiji.
Dangane da batun da wasu jama'a ke yi na cewar tsabar ilimin Boko da wayewa gami da daula shi ya sabbaba faruwar wancan iftila'in, Maryam Yahaya Sani ta bayyana cewar ko kadan batun ba haka ba ne, ilimin Boko ko wayewa ko wata gata ba ta sanya wa zuciya ta bushe har akai ga kisan Miji, abinda Maryam ta aikata ta ta nunawa Duniya matsayin ta na wacce bata samu tarbiya ba da ilimin addinin Musulunci.
Bisa ga fargaba da wasu magidan ta suka samu ta fuskar tunanin karin Aure sakamakon faruwar wannan al'amarin, Shugabar ta Ummul Khairi ta bukaci Maza da kada su shiga cikin rudani domin ba a taru an zama daya ba, inda ta bukaci iyaye Maza da Mata su dage wajen kula da tarbiyar 'ya'yan su ta hanyar sanya su a makarantun addini, kuma Maza duk wanda ke da hali na karin aure don Allah yayi kokari ya kara, domin kulle kofar faruwar wata fitina da ka'iya zuwa ta dalilin rashin auren Matan.
Copy the link below and Share with your Friends:
No comments:
Post a Comment