SANIN kowa ne cewa tuni fitacciyar mawak'iya Binta Labaran, wadda aka fi sani da Fati Nijar, ta rikid'e ta zama jaruma kuma furodusa a Kannywood. Fati ta shirya finafinai da dama.
To sai dai kuma tun daga lokacin da ta fara shirya finafinan nata yau kusan shekara biyu kenan, fim d'aya ne kawai ya fito kasuwa, wato ‘Sakatariya’, wanda ita ce jarumar fim d'in.
Irin bajintar da ta nuna a fim d'in ya sa ana ganin hakan zai kai ta ga matsayin da ta ke buri na zama fitacciyar jaruma, to kuma sai abin ya zama ba hakan ba; Fati ba ta k'ara fitar da wani fim ba.
Hakan ya sa ana tambayoyi a bayan fage: shin wai karaya ta yi ne ko kuma wani dalili ne ya sa ta jingine aikin?
Wakilin mujallar Fim a Kano ya nemi jin ta bakin jarumar, inda ta amsa wannan tambayar da ma wasu.
Ga tattaunawar tasu:
FIM: Hajiya Fati Nijar, kusan shekara biyu kenan tun da ki ka tsunduma cikin harkar shirya fim da fitowa a fim.
A lokacin da ki ka fara, kin bugi k'irjin cewar za ki shirya finafinai masu yawa a kamfanin ki na Girma-Girma, to sai dai daga lokacin zuwa yanzu fim d'aya ne ki ka fitar.
Ko dai kin karaya ne?
FATI NIJAR: To gaskiya ba karaya na yi ba, kawai dai an d'an samu jinkiri ne ban k'ara fitar da wani ba, shi ne ake ganin kamar na karaya.
Masu kallo su zuba ido, nan gaba kad'an za su ga finafinai na da na shirya zan fito da su, kuma akwai wad'anda na ke shirin yi nan gaba kad'an, irin ‘Kasada’ da kuma ‘’Yar Maiganye’.
Sannan kuma akwai shirin da na ke yi na yin finafinai masu dogon zango, irin wad'anda ake nunawa a manyan gidajen talbijin a yanzu.
FIM: Rikid'ewar da ki ka yi daga mawak'iya zuwa jaruma ta mayar da ke wata Fati Nijar ta daban.
Ko yaya ki ka ji da ki ka samu kan ki a haka?
FATI NIJAR: To ni dai gaskiya ban ji komai ba, amma dai zan iya cewa na samu d'an canjin yanayi saboda a matsayi na na mawak'iya kuma na koma ina yin aktin duk da cewa akwai bambanci sai dai ba wani yawa ba ne.
FIM: Bayan kasancewar ki jaruma, sai ya zama ke ce mai shirya fim d'in.
Yin hakan bai sa aiki ya yi maki yawa ba?
FATI NIJAR: Ai ina ganin abin duk d'aya ne, mawak'i ma zai iya zama furodusa kuma jarumi. Wannan ne ma ya sa na ga ya kamata na rink'a yin furodusin, ba wai na tsaya kawai a wak'a ba.
FIM: Ita harkar furodusin a masana’antar fim yadda ta ke daban da yadda ake kallon ta.
Ko yaya ki ka samu kan ki a matsayin ki na furodusa?
FATI NIJAR: A gaskiya akwai wannan. Ka san yadda harkar mutane ta ke, ba za ka iya gane halin mutum ba sai lokacin da harka ta had'a ku, don akwai rashin gaskiya sosai a wajen mutanen mu. Sai ka ga su na ta yi maka dad'in baki, amma daga ka shiga hannun su, to sai dai Allah Ya fitar da kai.
FIM: A fim d'in ki na farko, ‘Sakatariya’, kin nuna jarumtar da masu kallo su ke ganin kin burge su. Ko yaya ki ke kallon wannan nasarar da ki ka samu a fim d'in?
FATI NIJAR: To haka ne, don wasu jama’a da dama sun ji dad'in aktin d'in da na yi, har ma su na cewa ai tun tuni ya kamata a ce na fara, wasu kuma su na cewa ya kamata na tsaya a wak'a ta.
Ka san mutane kowa da yadda ya ke kallon rayuwa, kuma da man shi fim d'in da na fara yi na fara ne don na samu wata k'warewa a harkar, kuma na yi koyi da sauran mawak'a na duniya; domin idan ka kula da yawa fitattun mawak'a na duniya za ka ga su na yin fim.
FIM: Kin tab'a fad'a mana cewar ki na so ki zama jarumar da ta sha gaban duk wata jaruma a harkar fim.
Ko har yanzu ki na da wannan buri?
FATI NIJAR: In-sha Allahu kuwa! Burin ya na nan, kuma da yardar Allah zan cika burin nawa.
FIM: Salon fim d'in ‘Sakatariya’ ya bambanta da sauran finafinai ta sigar labari da kuma tsari. Me ya sa ki ka d'auki wannan salon?
FATI NIJAR: Haka ne.
Ka san duk finafinan mu yawancin su labarin duk iri d'aya ne, kuma jigon su soyayya. Duk da ba laifi ba ne a nuna soyayya a fim, amma dai bai kamata ta rink'a zama ita ce jigon labari ba.
To ni gaskiya ina so na kawo canji ne a masana’antar mu ta fim ta hanyar kawo abubuwan da ba a yin su a ciki.
FIM: To da wak'a da fim wanne ya fi cin lokaci?
FATI NIJAR: A gaskiya wak'a ta fi cin lokaci, saboda shi fim magana ce , kuma kafin ka fara sai ka haddace, amma ita wak'a sai ka tsaya ka yi tunani a k'wak'walwar ka. Sannan sai ka shafe tsawon sa'o'i uku ka na cikin situdiyo.
Amma shi fim za ka iya yi a cikin minti talatin, idan an gama sin d'in ka ka yi tafiyar ka.
FIM: Ganin jarumtar da ki ka nuna a ‘Sakatariya’, an yi zaton za a rink'a ganin ki a sauran finafinai na wasu kamfanoni, amma sai ba a ga hakan ba.
Ko dai kin tsaya ne a na kamfanin ki kawai?
FATI NIJAR: To ya danganta dai, don gaskiya ina da k'arancin lokaci ne, amma dai ana kawo mini aikin sai dai rashin lokaci, sai dai ina sa ran nan gaba kad'an zan rink'a ware lokaci na yin fim wanda zai zama ko wata shida ne a cikin shekara, don ya zama na samu damar yin finafinai har ma wad'anda ake gayyata ta.
FIM: A yanzu dai ki na nufin k'ofa a bud'e ta ke ga duk wanda zai gayyaci Fati Nijar aiki matuk'ar ya dace da ita?
FATI NIJAR: E, gaskiya haka ne.
Duk wanda ya ke ganin na dace da fim d'in sa, to ya na iya zuwa ya same ni mu daidaita. Sai dai kuma kamar yadda na fad'a maka, ina da k'arancin lokaci, amma dai hakan ba zai hana ni na yi fim ba.
FIM: Daga yadda ki ka kalli harkar fim bayan shigar ki, ki na ganin nan gaba akwai nasara?
FATI NIJAR: E, gaskiya za a iya cin nasara, amma dai sai an cire son zuciya, don gaskiya harkar fim mu na da buk'atar gyara sosai, kuma babbar matsalar da ta kashe harkar ita ce ba ma karb'ar gyara a daidai lokacin da ya dace, sai abu ya b'aci sannan za a zo ana yin kame-kame.
FIM: A yanzu harkar fim ta na cikin wani hali ta fuskar kasuwa.
Me ki ke ganin ya kawo hakan?
FATI NIJAR: Gaskiya yanayin finafinan mu ne. Da kamar a ce mu na yin finafinai irin yadda ya dace da rayuwar mu, to da ba za a samu kai a cikin yanayin da ake ciki ba a yanzu.
FIM: Menene ya fi ba ki sha’awa game da harkar fim?
FATI NIJAR: To ka san ita harkar fim akwai nishad'i a cikin ta, kuma shi d'an’adam kullum ba abin da ya ke so kamar ya samu kan sa cikin nishad'i.
Don haka na kan samu kai na cikin farin ciki idan mu ka had'u a wajen lokeshin mu na wasa da dariya.
FIM: A matsayin ki na jaruma, wace shawara za ki ba abokan aikin ki?
FATI NIJAR: To gaskiya shawarar da zan bayar ita ce su zamo masu gaskiya da kamun kai, musamman ma mata, saboda wani lokacin idan mace ta na kama kan ta sai a ce ta na da girman kai, to ba girman kai ba ne.
Don haka mata ya kamata su gane matsayin su na ’ya’ya mata; ba ko’ina za su rink'a zuwa su na yin abu kai-tsaye ba.
Don haka mata mu tsare mutuncin mu.
Daga mujallar fim
Copy the link below and Share with your Friends:
No comments:
Post a Comment