Irin wadannan ke batawa hukumar yansanda suna - NewsHausa NewsHausa: Irin wadannan ke batawa hukumar yansanda suna

Pages

LATEST POSTS

Sunday 19 November 2017

Irin wadannan ke batawa hukumar yansanda suna

Irin wadannan ke batawa hukumar yansanda suna....

Barau Garba jami'i ne dake aiki karkashin hukumar yansandan kwantar da tarzoma (Mopol), to amma ya manta aikin da ya kamace shi na kwantar da tarzoma yana kokarin tadata.

Yarinya ce yar shekara 14 aka aika da kudi, cikin rashin sa'a ta yada kudin a motar da ta shiga. A kokarinta na neman motar da ta shigo ne ta hadu da wannan jami'i, inda ya nuna zai taimaketa, bayan ta labarta masa abinda ke faruwa, ta kuma sanar dashi cewa yanzu ko kudin komawa gida batadasu, inda ya nuna zai taimaketa ya mayar da ita gida, amma sai yaudareta ya tafi da ita ya rufe a dakinsa, yayi ta cin zarafinta har tsawon kwana 6, inda yaji mata raunuka masu munin gaske a sassan jikinta.

Dayake abin yafaru ne a jahar Delta,shi kuma Barau dan asalin jahar Sokoto ne, ita kuma Maryam yar asalin jahar Kano ce, shine jami'an wannan gari da abin yafaru suke ta bawa iyayen yarinya shawarar su rufe maganar, domin idan ta bayyana sune zasuji kunya, kasantuwar duk daga yankin arewacin kasar nan suka fito.

Wannan ba karamin zalunci bane, lalle yakamata hukuma tayi bincike kan wannan lamari, kuma Barau ya fuskanci hukuncin abinda ya aikata, domin ya zama izina ga duk mai yunkurin aikata hakan anan gaba...!!!

Suma iyaye yakamata su kiyaye wajan aiken yayansu masu kananun shekaru, musamman ma mata, domin kaucewa bata gari irinsu Barau.

Nan kasa hoton Barau ne da kuma takardar asibitin da aka duba Maryam.


              Post by Nura Pro Brilliant

Copy the link below and Share with your Friends:

Download Our Official Android App on Google Playstore HERE
OR
Download from another source HERE



No comments:

Post a Comment