Sarkin Kano ya bi sahun Dangote, Ya bayar da shawarar sayar da kadarorin gwamnati - NewsHausa NewsHausa: Sarkin Kano ya bi sahun Dangote, Ya bayar da shawarar sayar da kadarorin gwamnati

Pages

LATEST POSTS

Thursday 22 September 2016

Sarkin Kano ya bi sahun Dangote, Ya bayar da shawarar sayar da kadarorin gwamnati

Mai Martaba Sarkin Kano, Alhaji Muhammad Sanusi II ya jaddada cewa dole Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sayar da hannayen jarin gwamnati da ke kamfanonin mai da kuma yin gwamjon matatun mai idan har yana son farfado da tattalin arzikin Najeriya.

Ya kara da cewa ta haka ne kadai gwamnati za ta samun kudaden da za ta aiwatar da manyan ayyuka tare kuma da farfado da darajar naira. Ya ci gaba da cewa idan har kuma za a sayar da kadarorin, gwamnati ta yi tsari ta yadda za ta iya karbar kayanta daga baya.
A baya-bayan nan dai shugaban Babban Bankin Nijeriya (CBN), Dr. Godwin Emefiele ya dora alhakin faduwar darajar Naira wadda ta Jefa kasar nan cikin halin kunci a kan tsoffin shugabannin Bankin biyu, Sarkin Kano, Mai Martaba Muhammad Sanusi II da kuma Farfesa Chukwuma Soludo bisa yadda suka salwantar da kudaden ajiyar waje na Nijeriya.
A cewarsa, a lokacin da mutanen biyu suka rike shugabancin Bankin, farashin gangan fetur ya kai dala 110 kuma Nijeriya na da isassun kudade a asusun ajiyarta ta yadda za ta iya amfani da kudaden wajen gudanar da manyan ayyuka.
Haka nan kuma Shugaban Bankin ya tabbatar da cewa Nijeriya na gab da ficewa daga yanayin kuncin da ta samu kanta inda ya fayyace matakan da gwamnati ta dauka wanda ya hada da gabatar wa majalisar dokoki kudirin gaggawa na farfado da tattalin arziki.
Ya ci gaba da cewa masu zuba jari daga waje su saka dala Bilyan daya a Harkokin tattalin arzikin Nijeriya sannan kuma a cikin wannan mako gwamnatin tarayya za ta saki Naira Bilyan 374 don gudanar da manyan ayyuka sai kuma rancen kudi da za a baiwa ‘yan kasuwa su milyan daya yana mai cewa gwamnati za ta fara bayar da Tallafin dubu biyar ga wasu kebantattun mutane kamar yadda ta yi alkawari.


Copy the link below and Share with your Friends:

Download Our Official Android App on Google Playstore HERE
OR
Download from another source HERE



No comments:

Post a Comment