Siyasa da tattalin arzikin arewacin Najeriya bayan yanci kai - NewsHausa NewsHausa: Siyasa da tattalin arzikin arewacin Najeriya bayan yanci kai

Pages

LATEST POSTS

Sunday, 18 September 2016

Siyasa da tattalin arzikin arewacin Najeriya bayan yanci kai

– A ranan 1 a watan Oktoba, anyi bikin yancin kan Najeriya daga karkashin mulkin shugabannin Birtaniya
– A wannan ranan ne, Firimiyan Arewacin Najeriya, Alhaji Sir Ahmadu Bello Sardauna na jam’iyyar NPC yayi gamayya da jam’iyyar NCNC
Bayan yan ci kai, ya cigaba da kasancewa firimiya har kisar sa a shekaran 1966.
Bayan kisan gillan da Manjo Janar Kaduna Nzeogu ya masa a Kaduna, arewacin Najeriya ta shiga wani halin ni ‘yasu a siyasance da arzikince. Zamuyi bayanin siyasan arewacin Najeriya da tattalin arzikin ta bayan samun yan cin kai.
Siyasa
Gwamnatin soja ta cigaba da mulki har shekaran 1978. A shekarar 1979, Malam Aminu Kano ya shugabanci jam’iyyar the Peoples Redemption Party (PRP) wajen kwato mulki a hannu gwamnati mai ci ta National Party of Nigeria (NPN) kuma PRP ta lashe zaben takaran gwamna a jihar Kano da Kaduna, haka zalika jam’iyyar PRP ta lashe kujerua da dama a majalisar dattawa,da majalisar wakilai ,da kuma majalisan dokokin jiha. Inda aka gudanar da zabe cikin zaman lafiya da lumana.
Bayan sun lashe zaben arewa ,Mallam Aminu Kano ya bayyana a jawabin da ya gabatar a ranan kaddamar da jam’iyyar PRP a watan Nuwanban 1978 a jihar Legas cewa wadanda suka fi amsa kiran garambawul yan yankin arewa maso yammacin Najeriya ne.
A jihar Kaduna, Alh Abdulkadir Balarabe Musa, shine mutum na farko da yayi mulkin gwamnan jihar kaduna a demokradiyyance, ya fada a ranan 2 ga watan Oktoba 1979, ranan aka anstar da shi cewa, gwamnatin PRP ta zo tayi gyara a arewacin Najeriya.
A jihar Kano kuwa, Alh Mohammadu Abubakar Rimi ne ya lashe zaben karkashin jam’iyyar PRP wanda ya taka rawan gani a bunkasa ilimi, raya karkara, aikin noma a arewacin najeriya.
Jam’iyya PRP a lokacin ta hada kai da sauran jam’iyyun siyasa a arewa domin yaki da gwamnati mai ci a sama National Party of Nigeria (NPN), yayinda ta hada kai da Great Nigeria Peoples Party (GNPP) ,Nigeria Peoples Party (NPP) da Unity Party of Nigeria (UPN) kuma sun fara hakan.
Amma kac! Hannun agogo ya koma baya ne a ranan 7 ga watan mayu 1981, inda majalisar dokokin jihar kaduna wacce yan jam’iyyar adawa a jihar ta NPN ne ke da rinjaye, suka nada kwamiti tare da goyon bayan gwamnatin tarayya suka tsige Alh Abdulkadir Balarabe Musa a ranan 23 ga watan Yunin 1981.
Daga baya kuma gwamnatin NPN ta sa aka damke Dr Bala Usman, sakataren gwamnatin jihar Kaduna saboda ya raba wata takarda me kunshe da rubutu wanda aka yima taken ‘Ka biya haraji’?
Bata kare a jihar Kaduna ba, a jihar Kano, ranan 10 ga watan Yulin 1981, wasu yan daban da ake zargin jam’iyyar NPN ne ta turo suka kashe Dr Bala Mohammed, mai baiwa gwamnan jihar Kano shawara kuma suka kona gawarsa.
Daga baya a shekarar 1983 aka gudanar da zabe inda Alh Shehu Shagari ya lashe zaben shugaban kasa karkashin jam’iyyar NPN. Nasarar zaben ke da wuya, Birgediya janar Sani Abacha ya sanar da juyin mulkin Shehu Shagari karkashin jagorancin Janar Muhammadu Buhari saboda rashawa da almundahana da tayi kamari a gwamnatin Shehu Shagari.
Daga baya kuma dara ta ci gida inda janar Badamasi Babangida yayi juyin mulkin Buhari a shekarar 1985 kuma ya mika gwamnati ga Janar Sani Abacha a shekarar 1993 bayan ya soke zaben Abiola a ranar 12 ga watan Yuni.
Dawowan demokradiyya kasan gaba daya a shekarar 1999 inda jam’iyyar PDP ta tsiro, siyasa a arewcin najeriya bata haifi da ai ido ba. Duk da yunkurin kungiyar Movement for democracy and justice MDJ karkashin MD Yusuf and Alh Abdulkadir Balarabe Musa, jam’iyyar PDP bata gushe tana samun nasara a fadin arewa ba.
A yau bayan shekaru 16 da gwamnatin fara hula, inda gwamnonin arewacin Najeriya ke amsan makudan kudi domin bunkasa kiwon lafiya jama’an su amma kac! Albasa batayi halin ruwa ba. Innama babakere da kunduguzu suke yi da dukiyoyin jama’a. Hakan ya sanya siyasar arewa cikin halin kakanikaye, yunwa, talauci, jahilci yayi jama’an arewa katutu.
Tattalin arziki
Arewacin Najeriya wacce ke da jama’a 75 million ta fuskanci tabarbarewan tattalin arzikin ta saboda dalilai da dama
Hakikanin gasiya shine, arewacin Najeriya na da filin noma mafi girma amma saboda rashin shugabanni na kwarai bayan rasuwan su Sir Ahmadu Bello Sardauna, Sir Abubakar Tafawa Balewa, da sauran su, ya sa tattalin arzikin arewacin Najeriya na a tabarbare.
Duk da cewan arewa na da yawan jama’a, rashin ilimi da jahilci yayi mana katutu a zuciya sanadiyar rikon sakeni kasha da shugabanni sukayi kuma sukeyi. Abu maficin zuciya da ban takaici shine halin talaucin da jama’an arewa ke fama da shi.
Lissafin kwararru ya nuna cewa darajar talauci a jihohin arewa ya karu da kasha 80%. Cibiyoyin kasuwancin arewa (Kano da Kaduna) sunyi kasa a guiwa,kana wadansu su sun zama kayan tarihi.
Kamfanin masaka, hada motoci, kayan kwalba da ke baiwa tattalin arzikin arewan armashi a shekarun 1970 da 1980 a jihar Kaduna, sun mutu wanda yayi sanadiyar rashin aikin yi ga dubunnan mutane.
Noman gyada da auduga a yankunan jihar Kano, wannan shine mabibiyar harajin arewacin Najeriya, hakan ma’adinai a yankunan Flato da Benuwe da kuma wasu kamfanonin karafuna da ke yankunan Sakkwato.
Kamfanonin siminti a jihar Bauchi da Sakkwato da kuma kamfanin leda a jihar Kano. Wadannan sune ginshikin tattalin arzikin arewa wanda a yanzu, abin sai kuka.


Copy the link below and Share with your Friends:

Download Our Official Android App on Google Playstore HERE
OR
Download from another source HERE



No comments:

Post a Comment