‘Yan Majalisar Dattawa ba su amince da Shugaba Buhari ba - NewsHausa NewsHausa: ‘Yan Majalisar Dattawa ba su amince da Shugaba Buhari ba

Pages

LATEST POSTS

Tuesday, 27 September 2016

‘Yan Majalisar Dattawa ba su amince da Shugaba Buhari ba

– ‘Yan Majalisar Dattawan Kasar nan ba su yi na’am da tsarin Shugaba Muhammadu Buhari ba, na saida kadarorin Kasar
– Sanatocin Kasar sun ce a dai san yadda za ayi a fita daga kangin tattalin arzikin da ake ciki ba tare da an saida manyan kadarorin Kasa ba
Majalisa Dattawar Kasar ta bayyana wannan ne a zaman ta na jiya, Talata

A zaman ‘Yan Majalisar Dattawan Kasar nan a ranar, Talata 27 ga watan yau sun ce ba su amince da maganar sayar da manyan kadarorin Kasar ba, saboda radadin tattalin arzikin da aka shiga ciki. Shugaban Majalisar, Bukola Saraki ya yaba da kokarin ‘Yan Majalisar da gudumuwar da suka bada wajen muhawar game da batun.
Shugaban Majalisar Bukola Saraki ya bayyana cewa su dai sun yi irin na su rawar wajen ganin Najeriyar ta fita daga halin da ta shiga ciki na durkushewar tattalin arziki. Majalisar za tayi aiki tare da masu zartarwar wajen shawo kan matsalar da aka shiga. Shugaban Majalisar dattawar, Bukola Saraki yace za suyi aiki hannu da hannu tare da Shugaba Buhari wajen bada shawarwari da zantar da dokokin da suka dace, abin da Saraki ya kira alfanun Damukaradiyya
Majalisar Dattawar tace tayi nata kokarin wajen kawo karshen matsalar durkushewar tattalin arzikin Kasar. Haka shima Tsohon Shugaban babban bankin Kasar yace idan har aka samu damina mai kyau, to za a fita daga kangin da aka shiga a Kasar.
A jiya ne kuma dai Majalisar ta rantsar da sababbin ‘Yan Majalisar guda biyu, daga Yankunan Kogi da kuma Imo.


Copy the link below and Share with your Friends:

Download Our Official Android App on Google Playstore HERE
OR
Download from another source HERE



No comments:

Post a Comment