Tonan asiri: Dalilin da yasa kasar Najeriya ke da lalatattun Shugabanni - NewsHausa NewsHausa: Tonan asiri: Dalilin da yasa kasar Najeriya ke da lalatattun Shugabanni

Pages

LATEST POSTS

Monday, 26 September 2016

Tonan asiri: Dalilin da yasa kasar Najeriya ke da lalatattun Shugabanni

Bankole yace Najeriya na fama da mummunan shugabanci saboda lalatattun malamai
Tsohon kakakin majalisar Wakilai yace makomar kasar nan baida kyau

Dimeji Bankole, tsohon kakakin majalisar wakilai, ya daura laifin matsalolin shugabancin Najeriya a kan lalatattun malamai.
Wannan yazo ne yayinda tsohon kakakin yace makomar kasar baida kyau, jaridar Vanguard ta ruwaito.
Dimeji Bankole, tsohon kakakin majalisar wakilai ya daura laifin matsalolin shugabancin Najeriya a kan lalatattun malamai
A cewar shi, lalatattun shugabanni dake kasar a yanzu, wanda lalatattun malamai suka karantar a shekarun baya ne.
Yace: “makomar kasar nan baida alamun kyau. Akwai babban matsala. Gwamnati bazata iya biyan albashi da fansho ba. Idan kasar ta lalace a yau. Idan muna da matsalar shugabanci, saboda lalatattun malamai ne. najeriya na bukatar gyara.”
Da yake Magana kan kalubalan da karatu ke fuskanta, Bankole yace: “A yanzu, samun shiga makarantun jami’a ko Poly, dole sai dalubai sun samu maki da ya kai 160 zuwa 180 ko sama da haka.
“Haka kuma idan mutun zai shiga makaranta koleji sai ya samu maki 130. Wannan na nufin cewa tsarin yana zaben marasa kokari sosai ya kuma horar da su a matsayin malaman yayanmu.
“Idan muna zaben marasa kokari don su horar da kuma karantar da dalibanmu, ta yaya zamu sa ran dalibanmu su zama masu manyan rabo, idan duk cikin tsawon lokacin da suka dauka sun karatu, an ware su daga masu ilimi sosai aka kuma ba’a tursasasu sun kai matsayin wadanda sun kuma wuce wadanda basu samu shiga jami’a ba?”
Ya kara da cewa: “A halin da kasar Najeriya ke ciki a yanzu daliban makarantunmu basu da kokari. Wannan babban matsala ne! Me yasa muka bari hakan na faruwa?
Wannan ba abun wasa mane. Makarantun kolejinmu ya zamana su ke da mafi yawan maki, ta yanda zai jawo hankalin dalibai masu hazaka , saboda suna da muhimmanci sosai ga makomar kasar nan.”


Copy the link below and Share with your Friends:

Download Our Official Android App on Google Playstore HERE
OR
Download from another source HERE



No comments:

Post a Comment