Jaridar Associated Press ta bada rahoton cewa gwamnatin tarayya ta kai karan manyan kamfananonin man kotu domin fitar da man fetur ba bisa doka ba kimanin kudi $12.7 billion tsakanin 2011- 2014.
Ma’aikatan Najeriya sun lakuto maganan AP cewa an fitar da tankunan mai ne ba bisa doka ba zuwa kasar Amurka.
Yanzu, wata babban kotun tarayya da ke zaune a legas zata fara amsa kara a mako mai zuwa akan kanfunan Chevron, British-Dutch Shell, Italian ENI’s Agip, France’s Total da Brasoil of Brazilian Petrobas.
Karar gwamnatin tarayya wacce lauya, Farfesa Fabian Ajogwu akan Chevron , wacce ta zo na farko da za’a gabatar 30 ga watan Satumba.
AP ta bada rahoton irin wadannan karar, cewa gwamnatin tarayya ta zargi kamfanonin mai da laifin kin bayyana sama da gangan mai 57 million . wannan lamban an same shi ne a rahoton kudi cewa an fitar da shi zuwa kasar Amurka
Wadansu abubuwa da akayi da suka sabawa doka ya kunshi kaya cike da jirgin ruwa. Sai a ce an dauka kaya kadan a Najeriya,ashe cike da jirgi aka dauka zuwa kasar Amurka.
AP ta bada rahoton cewa Micheal Kanko ya tabbatar da cewa wata manhajar yanar gizo lauyoyinsa sukayi amfani da shi .
No comments:
Post a Comment