Obasanjo yayi magana akan tabarbarewan tattalin arziki - NewsHausa NewsHausa: Obasanjo yayi magana akan tabarbarewan tattalin arziki

Pages

LATEST POSTS

Wednesday, 28 September 2016

Obasanjo yayi magana akan tabarbarewan tattalin arziki

Obasanjo ya tuhumci gwamnoni da laifin rashin tattali
– Tsohon shugaban yace duk da rashawan da ke gwamnatin sa,ba’a taba kudin fansho ba
A jiya ne 27 ga watan Satumba, tsohon Shugaban Kasa Olusegun Obasanjo ya tuhumci gwamnoni da laifin tabarbarewan tattalin arziki.
Obasanjo
Yace tsaffin gwamnonin sun bada gudunmuwa wajen kalubalen tattalin arziki da kasa ke fuskanta a yanzu sabida sun kasance suna fito na fito da shi lokacin y ace a dinga tattali lokacin da farashin mai ke da armashi.
Obasanjo yayi magana ne a taron Fanshon duniya a Abuja inda yace gwamnoni da dama ne suka hana shi yin tattali lokacin da kasa ke da ishasshen kudi. He said: “I remember when I was in government and I told, particularly, the governors, ‘please let us save for the rainy days.’ They said no!
Yace: “Na tuna lokacin da nike gwamnati, a fada ma gwamnoni ,mu dinga tattali, sukayi kunnen kashi!”
Lokacin akwai kudi, yanzu da babu; babu inda mukayi tattalι
Bayan haka, Obasanjo ya yabi yadda ake gudanar da fansho. Yace duk da cewan an dau shekaru ana rashawa a najeriya, ba’a taba kudin fansho ba.
“Daya daga cikin abubuwan da nike farin ciki da su shine a shekaru biyar,lokacin da komai na kudi ana babakeren, ba’a taba kudin fansho ba. Ina da fahimtar kudin fansho wani abu ne da ya wajaba muyi tattali.”
A watan agustan 2016, Najeriya ta shiga cikin wata halin tabarbarewan tattalin arziki a lokacin na farko cikin shekaru 20. Ana jingina tabarbarewan ga hare-haren yan bindigan Neja delta key i akan kafufuwan man fetur.


Copy the link below and Share with your Friends:

Download Our Official Android App on Google Playstore HERE
OR
Download from another source HERE



No comments:

Post a Comment