Abunda wani Alhaji yayi wa wannan matashiyar yarinya a jihar Sakkwato zai sa ka zubar da hawaye (Hoto) - NewsHausa NewsHausa: Abunda wani Alhaji yayi wa wannan matashiyar yarinya a jihar Sakkwato zai sa ka zubar da hawaye (Hoto)

Pages

LATEST POSTS

Wednesday 21 September 2016

Abunda wani Alhaji yayi wa wannan matashiyar yarinya a jihar Sakkwato zai sa ka zubar da hawaye (Hoto)

Wani dan jaridar Najeriya dake aiki tare da gidan radiyon DW na kasar Jamus, Faruk Muhammad Yabo, ya bayyana wani labara mai taba zuciya a shafin zumunta na Facebook.
Ya yada hoton wata matashiyar yarinya marainiya wacce ke dauke da cikin wata takwas (8) da wani Alhaji yayi mata a jihar Sakkwato. Karanta labarin a kasa

Marainiya Maimuna

“Labarin wannan matashiya mai karancin shekaru, Maimuna wacce ta kasance marainiya a kauyen Birnin ruwa dake jihar Sakkwato, wani Alhaji Giwa wadda suka fito daga kauye daya ne yayi mata fyade har ciki ya shiga, daga bisani ya tafi ya barta, labarin abun tausayi ne. maimuna dake dauke da cikin wata 8 bata da kowa da zai dauki nauyin cikinta a yanayinda take ciki na karanci shekaru. Yanzu bata da madafa tunda mahaifinta ya dade da rasuwa, kuma mutumimn da ake zargin yayi mata ciki ya karyata a gaban kotun shari’a na jihar Sakkwato cewa bashi yayi mata cikin ba, amma Maimuna ta dage kan cewa Alhaji Giwa ne yayi mata cikin.
“Masu bada shaida guda biyu wadanda suka fito daga kauye daya sun rantse a gaban kotu cewa Alhaji Giwa ya fada masu cewa zai dauki Maimuna ya kaita gurin gwani a fannin zubar da ciki, domin a zubar mata da ciki, amma daga baya ya canza ra’ayin sa. Yarinya talakawa, Maimuna ta na tsananin bukatar taimako daga hukumar kare hakkin mutane saboda Alhaji mutumin da yayi mata ciki ya rigada ya dauki Lauya kan shari’ar”
Abun tausayi!


Copy the link below and Share with your Friends:

Download Our Official Android App on Google Playstore HERE
OR
Download from another source HERE



No comments:

Post a Comment