Wani saurayi ya yi niyyar kashe budurwar sa sakamakon zata auri wani A Garin katsina - NewsHausa NewsHausa: Wani saurayi ya yi niyyar kashe budurwar sa sakamakon zata auri wani A Garin katsina

Pages

LATEST POSTS

Sunday 24 December 2017

Wani saurayi ya yi niyyar kashe budurwar sa sakamakon zata auri wani A Garin katsina

Wani saurayi ya yi niyyar kashe budurwar sa sakamakon zata auri wani

Rundunar 'yan sanda ta jihar Katsina ta yi nasarar cafke wani mai suna Abubakar Musa, dan shekaru ashirin da uku da haihuwa dake karamar hukuma Charanchi bisa zargin hallaka budurwarsa da suka kwashe shekaru biyar suna tare.

Da yake jawabi ga manema labarai, kwamishinan 'yan sanda na jihar Katsina, Benson D.

Gwana ya ce a bincike da rundunar ta gano Abubakar ya dauki A'isha Dikko a babur ya nufi dajin Tamawa da ke karamar hukumar Kurfi, inda ya fiddo wuka ya yi mata yanka rago, wanda a zaton sa ta mutu ya baro ta cikin jini. Ashe tana da sauran kwana.

utane sun zo wucewa suka lura da halin da take ciki suka yi gaggawar kai ta asibitin garin Kurfi, inda yanzu haka tana samun sauki.

RARIYA ta tambaye shi ko me ya sa ya aikata wannan mummunan aiki ga masoyiyar sa, ya ce saboda kaunar dake tsakanina da ita kwatsam sai na ji an ce za ta yi aure, shi ne na kudiri kashe ta har lahira. Amma dai yanzu yana da na sani aikata hakan.


Copy the link below and Share with your Friends:

Download Our Official Android App on Google Playstore HERE
OR
Download from another source HERE



No comments:

Post a Comment