Bayan ya samu kuri'u masu tarin yawa, Muhamed Salah ya doke dan wasan Gabon Pierre-Emerick Aubameyang da dan kasar Guinea Naby Keita da dan Senegal Sadio Mane da kuma dan Najeriya, Victor Moses.
Dan wasan mai shekara 25 ya shaida wa BBC cewar: "Na yi murnar cin wannan kyautar." "Mutum zai ji dadi na musamman idan ya ci wata kyauta. Za ka ji ka taka rawar gani a shekara, na yi murna matuka. Zan so in sake cin kyautar a shekara mai zuwa!" Salah, wanda ya fi kowa cin kwallo a gasar Firimiya da kwallayensa 13, ya taka rawar gani a wannan shekarar a kulob dinsa da kuma kasarsa.
A farkon shekarar 2017, shi ne ya jagoranci kasar Masar a lokacin da 'yan wasanta suka zo na biyu a gasar cin kofin nahiyar Afirka.
Daga baya a cikin wannan shekarar, dan wasan gaban mai yawan gudu, ya taka rawa a wajen cin dukkan kwallaye bakwai din da suka sa tawagar kasarsa, Pharaohs, ta samu zuwa gasar cin kofin duniya ta kwallon kafa a karon farko tun shekarar 1990 - ya tallafa wajen cin kwallo biyu kuma ya ci kwallo biyar, ciki har da fenareti na karshen da ya yi amfani da shi ya ci Kongo, lamarin ya sa kasarsa ta samu zuwa gasar ta Rasha. "Ina so na kasance dan Masar da ya fi fice saboda haka ina aiki tukuru," in ji mutumin da ya zama dan Masar na uku da ya ci kyautar kuma na farko tun shekarar 2008. "Ina bin hanyata kuma ina son kowa a Masar ya bi hanyata."
Copy the link below and Share with your Friends:
No comments:
Post a Comment