Hip Hop A Arewa Harka ce Ta Masu Ilmi ce Inji Naja'atu Janah - NewsHausa NewsHausa: Hip Hop A Arewa Harka ce Ta Masu Ilmi ce Inji Naja'atu Janah

Pages

LATEST POSTS

Friday 15 December 2017

Hip Hop A Arewa Harka ce Ta Masu Ilmi ce Inji Naja'atu Janah



Shahararriyar mawakiyar hip hop na harshen HausaNaja’atu wacce aka fi sani da Janah Stargurl, wacce ta yi wakar Godiya da Takama da kuma Lokacinmu ne, ta fadi abubuwa da dama masu mahimmanci da suka shafi harkan hip hop a Arewa, inda take ba ‘ya’ uwanta mawaka shawara kan cewa in za su yi waka su daina yi wa junansu habaici ko zage-zage, domin kuwa waka hanya ce na isar da sakonin alheri. 

Da farko dai za mu so mu san cikkakken sunanki?

Cikakken sunana shi ne Naja’atu Suleiman, Amma yanzu mutane suna kira na da Janah wasu kuma su ce Stargurl.

Ko za ki ba mu takaitaccen tarihinki?

Da farko dai an haife ni a Kano a wata unguwa mai suna Birgade, na yi firamare da sakandire a Birgade. Daga nan ne na fara Sa’adatu Rimi  College wanda har yanzu dai nake zuwa.

Me ya ja hankalinki kuma ya birge ki kika fara harkan Hip Hop?

To abin da da ya fara jan hankalina game da hip hop shi ne waka hanya ce ta isar da sako, kuma daman tun farkon taso wa ta, rapping na matukar birge ni, sai na ga me zai hana ni ma in gwada,  sai na fara da rubutun waka irin ta hip hop, na rubuta wakoki da dama, sai kuma maganar makaranta ya shiga gaba, daga nan ne na dakatar da waka, daga baya kuma da na ci gaba sai na zo har na shiga studio. Kamar yanda na fada a baya akwai wasu hanyoyi da mutun zai bi ya isar da sako, hip hop harkar ilimi ce saboda har wanda ba ka taba tinani ba sai ka ga sun saurare ka. Sabanin harkan hip hop babu wannan damar.
To yanzu akwai kungiyar da kike aiki da su ne?

Eh Janah ba ta da kungiya sai dai kungiyar da nake karkashi wato Yc2krecord.

Kawo yanzu kin yi wakoki kamar nawa?

Ina da wakoki akalla goma yanzu.

Kin taba yin album ne?

Gaskiya har yanzu dai ban saki album ba amma insha’allah ina da burin hakan a wannan lokacin.

A baya kin ce kin yi wakoki akalla guda goma, ko za ki iya kawo mana sunan wasu daga ciki?

Wakokina da suka fi suna su ne lokacinmu ne, da kuma nasara sai kuma takama da godiya.

A cikinsu wacce kika fi so?

Godiya, ina son takama amma ba ni kadai ba ce a ciki ni ma sani aka yi a ciki.

Akalla za ki kai shekara nawa da fara waka?

Gaskiya da fara wakata yanzu dai na kai shekara daya.

Wani irin kalubale kika fuskanta a harkarki ta waka?

Dama a rayuwa kome za ka yi sai ka fuskanci kalubale kala-kala, babban abin da na fi cin karo da shi shi ne mutane masu cewa in rasa abin da zan yi ina Bahaushiya sai hip hop? Toh wannan gaskiya yana daga cikin matsalolin da na ci karo da su, amma da yake akwai son abin a raina wannan bai sa na gaza ba,saboda haka nake jin ni yanzu ma na fara hip hop.

Kawo yanzu wadanne irin nasarori da ci gaba kika samu a harkan Hip hop?

Alhamdulillah ala kulli hallin, babu abin da zance wa Allah sai dai godiya saboda shi ne ya ba ni duk wani ci gaba da ake bukata a harkar. Misali a da in na je guri ba wanda ya san Janah amma yanzu kuma Alhamdulillah zan ga mutane sun zo ana maraba da zuwana guri. Ka ga wannan ma babban nasara ce.

Waye role model dinki?

3Dnatee.

A Cikin mawakan hip hop na duniya su wa suka fi birge ki?

Nicki Minaj da Lil Wayne da3Dnatee da Wiz Khalifah, gaskiya wadannan mutanen sun kasance mini tamkar madubi a fannin hip hop.

Wani mawaki kika fi kusanci da shi?

Chancy2 Mai gidana.

Wace kalar mota kika fi so?

Lambogini.

Wace kasa kike sha’awar zuwa?

Saudiyya da Amurika.

Wane Kalar abinci kika fi so?

Shinkafa da wake.

Wadanne irin abubuwa kike so ki ga kina yi a rayuwarki?

Burina na farko a rayuwa shi ne na ga na gina wata gidauniya ta taimaka wa mata ‘yan arewa musamman masu bukatar taimakon gagga wa.

Ko za ki iya gaya mana wane sako wakarki ta godiya take isarwa?

Eh to wakata  ta godiya ta kunshi sakonni da dama, in ka tsaya ka saurari wakar na yi ta ne a kan abubuwa da dama, amma  darasin da tafi koyarwa shi ne a kowane hali ka tsinci kanka ka gode wa Allah da dadi ko akasin hakan. Sannan da wasu a halittu da Allah ya yi, su kansu abin a tsaya a nazarta ne musamman in ka kalli yadda rayuwa take a yanzu. Wannan shi ne dalilin da ya sa na yi wakar godiya.

Wace shawara za ki ba ‘yan’uwanki mawakan Arewa?

Shawarata ga ‘yan’uwana mawaka musammam masu taso wa kamar ni, mu daina habaici ko zage-zage a waka, sannan kada mu ce mu dole sai mun zama wani abu, idan mu ka yi hakuri a sannun kunkuru zai je inda jirgin sama ya je.

Daga karshe me za ki ce wa masoyanki?

Masoya daman ai su ne komai, yau idan babu su ai ni ma babu ni, don haka naku na musamman ne. ina mika godiya ta musamman ga masoya a ko’ina ana tare, mu ci gaba da yi wa juna fatan alheri, ana tare iya wuya. Janah stargurl taku ce ina kuma matukar godiya da irin godummawar da kuka ba ni a rayuwa. Na gode.

Copy the link below and Share with your Friends:

Download Our Official Android App on Google Playstore HERE
OR
Download from another source HERE



No comments:

Post a Comment