A tattaunawa da tayi da PREMIUM TIMES HAUSA Umma tace shirya fim shine babban burin ta a rayuwa tun kafin ta shiga harkar fitowa a finafanai shine ta ga ta fara yin fim itama. ” Sunan fim dina dana shirya shine ‘Burin SO’. Na saka masa wannan suna ne ganin cewa kowa da yake soyayya burin sa a karshen wannan soyayya shine ya ga ya auri masoyin sa. Wasu kan dace da hakan ya wakana wasu kuma daga karshe abin sai ya zama labari.
Na zabi wannan suna ne domin in nuna irin halayyar da masoya kan fada idan suka sami kan su a cikin irin wannan hali. ” InshaAllah kamar yadda na sa rai fim din bazai wuce nan da watan gobe ko jiba, zai fito. Har yanzu ana aiki akai kuma in Allah ya yarda fim din zai burge.” Ummah ta kara da cewa, ta kashe kudi masu yawa wajen shirya fim din da ya shige miliyoyin naira. ” Na kushe kudi masu yawa amma kuma fa daidai karfi na ne. Wani abu da nike da yakini a kai shine zan yi iya kokari na domin ganin ya burge sannan duk abin da na samu a fim din zan gode wa Allah in mai da hankali kan na gaba.
Da aka tambaye ta game da wani hira da tayi da gidan Talabijin din Arewa 24 da ya bi duniya, umma tace bata so tayi maganar. ” Ba na so in yi wannan magana.
Tun bayan fitowar wannan hira da muka yi da Arewa 24, naji kalamai marasa dadi akan abin da na fadi a hirar. Sai dai abin da zan ce a nan shine kmar yadda na amsa tambayoyin da ya tambayeni cikin raha da barkwanci, hakan kawai bai isa ace wai shine dalilin da za a ce wai ban san addinina ba. Na abin da nake yi kuma Allah shine kadai masanin komai. Allah yakara mana sani da ya yi mana albarka gaba daya.”
Copy the link below and Share with your Friends:
No comments:
Post a Comment