Gashi Watan Rabiul Auwal ya kewayo ko me Mallam zai ce kan wannan wata?
Alhamudullah, da farko ina taya al’umman duniya murnar shigowar watan maulidi, watan murna, watan alheri, watan da aka haifi fiyayyen halitta, kowa na murna da wannan watan da Annabinmu ya zo a cikinta. Alhamdullahi sai mu kara gode wa Allah. Yadda muka ga farkonsa, Allah Ya sa mu ga karshensa lafiya, Allah kuma Ya sa mu samu dacewa da alhairai a cikinsa masu yawa. yanda watan ya saba zuwa mana da alherai ya kwaso mana ya kawo mana, muna fatan Allah zan kara mana wannan ni’imar, kuma muna rokon Allah Ya sa albarkacin wannan watan ya kawar mana da sharri da bala’o’i.
Wani dalili yasa akeyin wannan maulidin a duk shekara?
A dunkule dai maulidi nuna godiya ne ga Allah, da kuma bayyana murnarmu a fili da kuma boye. Allah Ya na cewa “Ku gode wa ni’imar Allah in da gaske kuke yi ku masu kadaita Allah ne masu bauta masa.” Babu wata ni’imar da ta zo duniyar nan da ta kai zuwan Annabi Muhammad (SAW) ‘Wa Ma Arsalnaka Illa Rahmatan Lil’Alamin’. A bisa haka muke nuna godiyarmu mu ga Allah a duk lokacin da watan ya zagayo. Manzon Allah ya shigo mana duniya ya zo ya yi shekaru 63 wato shekara 21 sau uku ko kuma shekara 7 sau tara.
Godiyarmu bata tsaya nan ba, muna kuma gode wa Allah da Ya sanya mu daga cikin wadanda suka yi imani da abin da ya zo mana da shi kuma muke bin tafarkinsa har muke raya watan da aka haifeshi da murna da kuma nuna soyayyarmu a fili da boye.
Akan zagaye gari har ma a zo a yi ta bukukuwa na raya maulidai a makarantu da kuma wurare daban-daban, ko akwai wasu abubuwa da aka fi son masu maulidi su maida hankali a kai ko kuma darasin da ake koya a ciki?
Daman ai irin wannan maulidoji da kuma zagayen gari, ana yinsu ne don nuna murnar, a nuna murnar a fili, amma idan aka zauna ba a yi wani abu ba ka ga ai ba a nuna murnar ba ke nan. Shi ya sa muke nuna murna a ko’ina, lungu da sako a yi wa Allah zikiri a kuma yi wa Annabi salati, a karanta Alkur’aninsa a kuma bayyana wa duniya tarihinsa don al’umma su san kyawawan dabi’unsa su kuma yi koyi da su. A lokacin da ake zagaya garin nan, ana murna da ranar haihuwar Annabi (SAW) mutumin da ba musulmi ba, idan ya zo ya tarar da babu wajen wucewa idan ya ce ‘What Happen’? Meye ke faru haka ne, sai a ce masa ‘Birth Day Celebration’ ne ake yi na Prophet Muhammad (SWA) zai kada kai ya ce au haka, ka ga shi an sanya masa wani karatu a kwakwalwa, zai kama tunanin cewar ashe haka Annabin nan yake a duniya. Daga nan zai tsunduma neman tarihin wannan Annabin, daga nan kuwa idan Allah Ya sa mai rabo ne sai ka ga ya ribanci wani abu na daga falalar Annabi tun da Manzon Allah rahama ne ga kowa da kowa, Rahamatul Lil-Alamina.
Shi Maulidin nan ma yanzu har cikin hutun gwamnati aka shigar da shi saboda muhimmancinsa, a da can baya ba a sanya ta ba; har hakan ya sanya wasu ke mamaki, wai me ya sa ake dakatar da aiki baki daya a ranar Maulidin Manzon Allah ne? To abin da ya faru ga wanda bai sani ba, bari na fada masa, a cikin alif da 1960 Shehu Ibrahim Kaulaha ya zo Najeriya ya sadu da Firayi Minista Abubakar Tafawa Balewa ya ce na zo na muku murna Najeriya ta samu ‘yancin kai. Banasare ya ba ku ‘yanci ya bar muku kasarku ta koma hannunku musamman kai da Nnamdi Azikwe kune Allah Ya baku Najeriya. Kai kana Firayi Minista, shi kuma yana Shugaban kasa, shi kirista ne kai musulmi ne, amma ina da labarin Dokta Azikwe yana zuwa coci ranar lahadi mulki bai hana masa ba, amma kai ma ina tsammanin mulkin ba zai hana maka zuwa juma’a ba ko? Ya ce masa yana zuwa har ma Shehu ya tambayeni yana zuwa sallar juma’a? na ce masa idan ya zo Bauchi muna kallonsa yana zuwa amma a Legos kam ban sani ba; sai ya ce masa kamar yadda kai kake zuwa Massalaci shi kuma yake zuwa Coci ga shi yana ba da hutu a ranar haihuwar Annabi Isa (a matsayin da shi aka daukeshi) wato ranar Kirsimeti, sai Shehu Ibrahim Kaulaha ya tambayi Tafawa Balewa cewar kaima kana ba da hutu ranar haihuwar Annnabinka Annabi Muhammad (SAW) sai Firay minista ya amsa da cewa a’a, sai ya ce wa Shehu ka shaida daga yau na shigar da hutun Maulidi Manzon Allah (SAW) cikin gwamnatin Najeriya kamar yadda ake shigar da Maulidin Annabi Isa a ciki a ba da hutu na musamman.
Daga wannan lokacin ne Maulidin nan ya zama na doka kowace gwamnati ta zo dole ta bi wannan dokar a ba da hutun aiki, tun daga gwamnatin Tarayya, Jihohi da na kananan hukumomi. Da kuma an bar shi ne kawai a hannun malamai, da Islamiyoyi. Shi Shehu ya ce dukkanin Idi na duniya, ba sai wani abu ya faru bane ake Idi? Misali in mako ya cika a ka zo jumma’a sai a yi idin juma’a, an ba da umurnin a yi azumi an samu an yi, washe gari sai a maida ranar na godiyar Allah, Idin karamar sallah ke nan ko, haka nan kuma Idin babbar Sallah kuma Allah Ya kira dukan jama’a na duniya musulmi kowa da kowa ya zo wajen da aka haifi Annabi Muhammadu, inda kuma aka saukar da Alkr’ani, shi ne ma’anar hajji, ziyarar inda aka haifi Manzon Allah shi ne ma’anar hajji da umura. Wannan dalilin ne ya sanya ranar tara ga watan zulhajji (ranar hajji ke nan) washe gari sai a kira duk duniya su yi wa bakin Allah yanka, sun sauko daga arfa a yi musu yanka na murna (layya ke nan) wannan ranar ta zama ranar godiya ga Allah.
Haka misali idan an haifi yaro akan yi suna a yi murna idan an bai wa mutum mukami ko sarauta yakan yi murna da bikin tunawa da ranar da aka ba shi wannan sarautar. “to ni a duniyar na duba ban ga wata ni’imar da ta kai zuwan Annabi (SAW) ba”. A sabili da haka ni a wajena babbar Idi ita ce ranar da aka samu Annabi Muhammad,” in ji Shehu Ibrahim.
A da can baya, mu a nan yankin Barebari bikin hawa suke yi duk shekara suna kiransa da suna Morekura, ta nan wajen mu kuma ana yin babban biki Daura da Gumel da sauran wurare haka kadan, daga baya sai ta nan muka fara yin bikin amma muna ce masa sallar kaza, a Kano kuma a ce Takutaha amma duk dai ana nuna murna ne da zagayowar ranar da aka haifi wannan Annabin wanda babu kamarsa.
Abun kamar wasa, sai abun ya tumbatsa yanzu ko’ina duk shekara sai an gudanar da maulidi a ciki da wajen kasar nan, lungu da sako.
Duk da hakan wasu na ganin maulidin da ake yi a matsayin Bidi’a wanda manzo bai yi ba, ba ka ganin kuna aikata abin ne a turbar bidi’a?
Ta yaya za a ce maulidi bidi’a? maulidi ai ba bidi’a ba ne. yanzu karamar misali da zan baka, dukanin ‘yan boko ba suna da ranar birthday dinsu ba? Su ba a yi musu wa’azi aka ce su daina ba sai a ce a daina na Annabi (SAW)? A idonmu muna gani idan gwamnati ta ba wani babban mukami, masoyansa sukan sa rana su je su taya shi murna, kuma in shekara ta zagayo su yi biki su sake murna, kamar na ga ana haka a Najeriya ko? Ko ba a yi ne?. A lokacin da aka zo yin wannan taron idan masoyansa suna son su yi taron, wasu kuma sai su gefe su ce maka kana musulmi ka yarda da wannan abun. Wai da wanda suka shirya maka taron da wanda suka ce kada a yi su waye masoyanka? Kila ma don masu mulki ne basu zuwa su ce musu bidi’a ne, ana ci a sha da su, na Manzon Allah ne bidi’a ke nan. Allah Ya sauwake.
Shin akwai ranar da ta kai ranar murna kamar ranar da Manzon Allah Ya ambata su Abubakar, Usman, Umar da Aliyu da sauran sahabbai ya ce musu dukaninku ‘yan Aljannah ne? Shin akwai ranar da ta kai wannan a wajen mutum ya yi murna? Amma sun yi biki? Don kawai mutum kalmar bidi’a bata masa wahalar fada. Duk wanda ya ce maulidi bidi’a ne mai muni tabbas lamarinsa abun tsoro ne, domin duk wanda ya ce Maulidi haramun ne to ba zai karanta Alkur’ani ba; matukar kuwa zai karanta to ya karanta maulidin Annabi , misali tun daga ranar da aka haifeshi har iya karshen rayuwarsa, da gwagwarmayarsa da dawowarsa daga Madyana, da fafatawarsa da karbar aiki da gwagwarmaya da Fir’auna da halakar da shi da sabuwar gwamnatin da aka samu bayan halakar da Fir’auna duk abun da ya faru har zuwa rasuwarsa har aka gama aka zarce aka yi maganar karuna. Duk wannan ba maulidin Annabi Musa aka yi ba? Ka duba suratu kasasu. Maulidin Annabi Musa, haka shi ma Annabi Isa tun daga kan kakarsa aka kawo maulidinsa da gwagwarmayarsa da bayansa da farko, dukkanin Annabawan nan sai ka karanta tarihinsu, za ka ji a cikin Alku’arni a na cewa karanta mana labarin Annabawa, na Annabi Muhmmadu din ne ba za mu karanta wa duniya ba? Duk wanda ya ce maulidi bidi’a ne ya ji kunya, ya ma daina karanta Alku’arni.
A karshe mene ne fatan Shehu Dahiru Bauchi?
Fatana dai Allah Ya fadakar da mu, ya kuma ganar da mu, tsakanin musulmi da maganar Annabi mutum ya maida maganar Annabi ta fi maganar kowa, aikin Annabi ya fi masa na kowa, sha’anin Annabi ya fi masa na kowa. Allah fa cewa ya yi “Ya kuma matan Annabi baku kama da kowa”. Kamar yadda matansa suka fi kowa babu wani abun da bai kamata na Annabi ya fi komai a wajenka ba. Don haka babu yadda za a yi ka soki wani abu na Annabi kuma ka zauna lafiya, hakan ba zai yiwu ba. Mu dai muna sake godiya da samun wannan Annabin Muhammad dan Abdullahi (SAW). Allah kuma Ya sa a gudanar da zagaye da sauran bukukuwan maulidin a dukanin fadin kasar nan da ma duniya baki daya. Allah kuma Ya sa mu dace da ceton Annabi Muhammadu, Ya kara mana soyayya a gareshi.
Copy the link below and Share with your Friends:
No comments:
Post a Comment