WASIYYA GA ANGO : Dabi'u Goma Da Ango Zai Mua'malance Su Domin Samun Zaman Lafiya Da Amaryarsa - Daga Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa - NewsHausa NewsHausa: WASIYYA GA ANGO : Dabi'u Goma Da Ango Zai Mua'malance Su Domin Samun Zaman Lafiya Da Amaryarsa - Daga Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa

Pages

LATEST POSTS

Friday 29 December 2017

WASIYYA GA ANGO : Dabi'u Goma Da Ango Zai Mua'malance Su Domin Samun Zaman Lafiya Da Amaryarsa - Daga Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa


Imamu Ahmad (RA) ya yi wa dansa wasiyya da wasu abubuwa guda (10) wadanda za su taimaka wajen zama da mace lafiya.

Yace ya kai da Na, hakika ba za ka taba samun jin dadin zamantakewar aure a cikin gidanka ba har sai ka kiyaye dabiu (10) da za ka mu'amalanci matarka da su don haka ka kiyaye su.

NA DAYA DA NA BIYU:
Hakika su mata suna son tausaswa da ja ajiki kuma suna son a dinga cewa ana sonsu ana kaunarsu. Don haka kada ka dinga yi musu rowar fadar haka, idan kuwa ka yi rowar to ka sanya hijabi tsakaninka da ita na samun Karancin soyayya da kauna.

NA UKU: Ka sani cewa su mata ba sa son mutum mai tsanani mai mugun takurawa, idan ka fahimce su, suna yiwa mutum rarrauna hidima. Don haka kowacce sifa ka ajiye ta a gurin data dace domin hakan shi zai fi jawo kauna da nutsuwa a tsakanin ku.

NA HUDU: Hakika su ma mata suna son irin abinda namiji ya ke so daga gurin mace, kamar daddadan kanshi, magana mai dadi, kyak-kyawar Shiga, tashin kanshi da dai sauransu. To don haka ka sifantu da dukkan wadannan halaye a dukkan yanayin ka.

NA BIYAR: Ka sani cewa Gida wata masarauta ce ta mace wadda take jin cikakken iko a cikinta kuma take jin cewa itace shugaba a cikinsa. To ina Jan kunnenka da Kada ka kuskura ka rusa wannan masarauta, kana mai Nuna mata cewa ita ba kowa bace ko kuma gidanka ne sai yadda ka so sai abinda ka so, idan kayi haka to ka tumbuke ta daga kan sarautarta, kuma mai mulki bashi da wani abokin gaba a Duniya fiye da Wanda ya sauke shi daga kan mulkin sa.

NA SHIDA: Dukkan mace tana son ta yiwa mijinta hidima amma kuma bata son ta rabu da 'Yan uwanta, to kada kayi kokarin raba ta da danginta ta hanyar bats zabin ko kai ko danginta, domin idan ta Zabe ka akan danginta to babu shakka zaka dawwama cikin bakin ciki da Bacin rai da za ka dinga samu daga gare su.

NA BAKWAI: Hakika ita mace an halicce ta ne daga kashin hakarkarin namiji karkatacce, wannan kuma ba aibu bane a gareta shi ne ma kuma sirrin kyawunta da kuma Jan hankalin da take yiwa maza, don haka kada ka hayayyaqo mata a lokacin da ta yi wani kuskure kana kokarin gyara ta ta karfin tsiya sai ka Karya ta, karya ta kuwa shine sakinta.

To kada kuma ka kyale ta tayi abinda taga dama ko kuma taci gaba da yin kuskuren, da sunan a karkace take, domin sai ta bijire maka daga karshe taki yi maka biyayya, kai dai ka kasance da ita baina baina.

NA TAKWAS: To kuma ka sani cewa su mata sun dabi'antu akan Kafircewa miji da yi masa butulci da kuma musun abin alheri. Idan da zaka kyautatawa mace tsawon shekara ko zamani sai wataran ka munana mata, za ta ce me ka taba yi min?. To kadaa wannan hali Nata ya sa ka kyamace ta gaba daya, domin idan ka kyamaci wannan dabi'ar daga gare ta to zaka yarda kuma da wasu halayen nata masu kyau.

NA TARA: Ita mace ba kamar Namiji bace, tana rayuwa ne cikin rauni na jiki dana ruhi, saboda haka ne ma Allah mds ya dauke mata wasu daga cikin farillan da ya wajabta mata a wadanban lokuta saboda wannan rauni na ta. Dubi yadda Allah ya dauke mata sallah kacokan a wannan yanayi ( na haila) ya jinkirta mata rama azumi har sai lafiyar ta ta dawo nishadinta ya daidaitu, to ka saukaka mata umarnika da hane- hanenka a wannan yanayi kamar yadda ubangijinta ya saukaka mata farillansa. 

NA GOMA: Ka sani cewa ita mace ribatacciyar baiwa ce a hannunka, don haka ka ji Kanta ka tausaya mata ka kuma dauke kai dangane da rauninta sai ta zamar maka kyak-kyawar abokiyar zama kuma mace ta gari.

Annabi (SAW) yace" Inai miku wasiyya da mata Ku rike su da alheri, domin ita mace an halicce ta ne daga kashi tankwararre kuma Mafi tankwarewar kashi shi ne sama , idan ka matsa sai ka tayar dashi to zaka karya shi, idan kuma ka barshi haka to zai dawwama a tankware kuma a karkace, to don haka inai muku wasiyya ta gari dangane da mata.

Kuma Annabi (SAW) yace" fiyayyenku shi ne fiyayyenku ga iyalansa kuma ni ne mafi alherinku dangane da iyalaina"

Allah ya bamu ikon zama da iyalan mu.

Daga shafin hukumar Hisba ta jihar Kano


Copy the link below and Share with your Friends:

Download Our Official Android App on Google Playstore HERE
OR
Download from another source HERE



No comments:

Post a Comment