Hadarin Butulci A Musulunci Daga sheikh Jabir sani maihula - NewsHausa NewsHausa: Hadarin Butulci A Musulunci Daga sheikh Jabir sani maihula

Pages

LATEST POSTS

Sunday 31 December 2017

Hadarin Butulci A Musulunci Daga sheikh Jabir sani maihula


Idan Allah ya hada ka da abokin zama, makwabci ne a unguwa ko wurin aiki, ko aboki ko abokin kasuwanci ko miji ko mata ko 'ya'ya  ko mahaifa, ko wani abu makamancin hakan, kamata yayi idan yayi ma ba daidai ba ka tuna alkhairan sa sai su mantar da kai sharrin sa. Babu wani abokin zama face yanada alkhairi da sharri. Idan aka tafiyar da zafin sharrin sa da sanyin alkhairin sa sai a samu Rayuwa Maidadi.

Babban Butulu shine wanda ya manta alkairan Allah na halittarsa da Allah yayi da bashi rayuwa da addini mai kyau da nunfashi da gani da ji da magana da sauran ni'iomin da basu kirguwa, amma kullun sai fadin sharri yake: akwai zafin rana, ba abinci, ba lafiya, ba ba ba....
Allah yana cewa, " [Ka ambaci lokacin] da Ubangijin ka yayi sanarwa: idan kuka gode zan kara muku, idan kuka butulce kuma lallai azaba ta mai tsanani ce."
Allah ya bamu ikon yafewa junan mu da godema ni'iomin sa.


Copy the link below and Share with your Friends:

Download Our Official Android App on Google Playstore HERE
OR
Download from another source HERE



No comments:

Post a Comment