'Akwai Yiwuwar Kwankwaso, Saraki, Goje, Wamakko, Amaechi Da Sauransu Za Su Koma PDP' - NewsHausa NewsHausa: 'Akwai Yiwuwar Kwankwaso, Saraki, Goje, Wamakko, Amaechi Da Sauransu Za Su Koma PDP'

Pages

LATEST POSTS

Monday 18 December 2017

'Akwai Yiwuwar Kwankwaso, Saraki, Goje, Wamakko, Amaechi Da Sauransu Za Su Koma PDP'


Hasashen mafi yawan 'yan Nijeriya na nuna cewa shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki, tsohon Gwamnan Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, Aisha Jummai Alhassan za su koma jam’iyyar PDP kafin babban zaben 2019.

A wani zaben jin ra’ayoyin jama’a na kwanaki biyar da kafar yada labarai ta Premium Times ta gudanar, fiye da mutane 700 suna da yakinin Sanata Saraki na iya komawa PDP.

A zaben jin ra’ayoyin an zana mutane 6 sannan aka tambaya waye jama’a suke gani a cikinsu zai iya komawa PDP.

Mutane 3,170 da suka kada kuri’a a inda kaso mafi rinjaye na kashi 22.6 (mutum 716) suka ce Mr. Saraki, zai koma PDP.

Wanda ke biye da Mista Saraki shine Rabiu Kwankwaso, tsohon Gwamnan Kano, wanda kashi 20.6 na masu kada kuriar (mutum 652) suka nuna fargaban Kwankwaso ma zai koma PDP.

Ministar mata, Aisha Al-Hassan, ce tazo na Uku da kaso 17.6 (kusan mutum 559) suka ce itama zata koma PDP.

Daya daga cikin wadanda jama’a ke ganin angulu za ta koma gidanta na tsamiya shine tsohon Gwamnan Sokoto, Aliyu Wamakko, wanda kaso 2.6 na masu kuriar (mutum 83) suke da yakinin shima zai koma PDP.

Sakamakon zaben kuma ya nuna akwai yiwuwar ministan sufuri kana tsohon Gwamnan Rivers, Rotimi Amaechi shima zai koma PDP. Kaso (7.7 mutum, 244) haka nan tsohon Gwmnan Gombe, Danjuma Goje, wanda kaso (5.5, mutum 175).

Kodayake dai dukkaninsu tsofaffin 'ya'yan jam’iyyar PDP ne amma kuma kimanin kaso 9.7 (mutum 308) sun kada kuri’ar cewa suna tunanin babu ko daya daga cikin mutanen da zai koma jam’iyyar ta PDP.

Copy the link below and Share with your Friends:

Download Our Official Android App on Google Playstore HERE
OR
Download from another source HERE



No comments:

Post a Comment