Ni Ba Cikakkiyar Budurwaba ce Amma kuma Ban Taba Aure ba inji Jaruma Rahama Sadau - NewsHausa NewsHausa: Ni Ba Cikakkiyar Budurwaba ce Amma kuma Ban Taba Aure ba inji Jaruma Rahama Sadau

Pages

LATEST POSTS

Monday 25 December 2017

Ni Ba Cikakkiyar Budurwaba ce Amma kuma Ban Taba Aure ba inji Jaruma Rahama Sadau

Rahotanni sun kawo cewa korarriyar jarumar kamfanin shirya fina-fina hausa na Kannywood, Rahama Sadau ta bai wa masoyanta damar yi mata tambaya a shafinta na twitter.

Wannan dama da jarumar ta bayar ya sa masoya na ta tururuwa wajen yi mata wasu tambayoyi da suka shafi rayuwarta.

Duk da cewa wasu daga cikin tambayoyin sun kasance masu nauyi jarumar tayi kokarin baar da amshoshin day a gamsar da masu yin tambayar ba tare da ta nuna dacin rai kan tambayar ba.



Shafin al’ummata ta wallafa tambayoyin da akayi wa jarumar da amshoshin da ta bayar kamar haka:

An tambayi jaruma Rahama ko ita budurwa ce gangariya:

Ga amsar da ta bayar “Ni budurwace, amma ba budurwa fil a leda ba, domin na rasa budurcina.”

An tambayeta wanda ya koyamata rawa?

Ta amsa cewa “Ali Nuhu.”

Me ta fi jin tsoro a duniya?

Ta ce “mutuwa.”

Yaushe za ta yi aure?

Ta ce “kwanannan,” amma bata bayyana ko wanene saurayin nata ba.



Shin za ta iya daina fim?

Ta ce “a’a.”

Dan wasan da ya fi birgeta a masana’antar fina-finan Hausa

Ta ce “Sadiq Sani Sadiq.”

Fim din da ta yi wanda ta fi so, ya fi birgeta

Ta ce fim din turanci na “Sons of the Caliphate”

An tambayeta ko shekarunta nawa?

Ta ce, “24.”



Copy the link below and Share with your Friends:

Download Our Official Android App on Google Playstore HERE
OR
Download from another source HERE



No comments:

Post a Comment