Amarya Tayi Yunkurin Yanka Angonta A Sokoto - NewsHausa NewsHausa: Amarya Tayi Yunkurin Yanka Angonta A Sokoto

Pages

LATEST POSTS

Wednesday 20 December 2017

Amarya Tayi Yunkurin Yanka Angonta A Sokoto

         
Wata Amarya a jihar Sokoto, mai suna Shafa Muhammad, yar kimanin shekaru 28, ta jiwa mijinta Umar Shehu rauni a kai bayan ta yanke shi da reza.

 Ma’auratan dai suna zaune ne a Unguwar Arkillar Liman, dake cikin karamar hukumar Wamakko a jihar Sokoto,lamarin ya faru ne a ranar Asabar da ta gabata 16 ga watan Disamba wanda yazo daidai da mako Uku da daura aurensu.

 Majiyarmu ta ce dama auren na dole ne akayiwa Shafa domin bata son wanda aka Aura mata din wato Umar Shehu.

Majiyar tace “Mijin nata ya je dakin amaryar tashi domin ganawa da ita amma tayi amfani da reza wajen kai masa hari har ta yanke shi a kai.”

 Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Sokoto, ASP Ibrahim Abarass, ya tabbatar da faruwar lamarin, sai dai yace an garzaya da mijin nata zuwa asibiti a inda akayi masa magani.

 Mista Abarass, ya kara da cewa yanzu haka Amaryar tana hannun hukumar yan sanda tana bincike kafin ta gurfanar da ita gaban kuliya.

 Sai dai kakakin yan sandan ya shawarci iyayen yara da su guji yiwa ‘yayansu auren dole.    

Copy the link below and Share with your Friends:

Download Our Official Android App on Google Playstore HERE
OR
Download from another source HERE



No comments:

Post a Comment