Muhimmiyar wasiyyatar Nafisat Abdullahi ga masu son koyi da ita a duniya - NewsHausa NewsHausa: Muhimmiyar wasiyyatar Nafisat Abdullahi ga masu son koyi da ita a duniya

Pages

LATEST POSTS

Saturday 9 December 2017

Muhimmiyar wasiyyatar Nafisat Abdullahi ga masu son koyi da ita a duniya


Gogaggiyar jarumar nan ta wasannin fina-finan Hausa a masana'antar Kannywood ta yi nasiha ga masoyan ta mata musamman ma masu so su yi koyi da ita a ruwar duniya ganin yadda ta samu nasarori da dama a harkar fim tare da lashe kambun kyaututtuka da dama.

Jarumar dai tayi wannan nasihar ne ga dumbin masoyan nata ne yayin da take fira da majiyar mu jim kadan bayan ta amshi kyaura jarumar-jarumai a fina-finan kasashen Afrika a wajen wani bikin karramawa da aka yi a birnin Landan a cikin watan da ya gabata.

Kannywoodscene  dai ta samu cewa da aka tambaye ta ko meye shawarar ta ga mata musamman ma masu sha'awar sana'ar fim din da kuma suke kallon ta a matsayin wata abar koyi a duniya, sai ta kada baki tace tana shawartar su da su kasance kan su kawai ba tare da kwaikwayon kalar rayuwar wasu ba.

A cewar ta, dukkan wadda ta ke so ta zama tauraruwa to dole ne ta guji kwaikwayon rayuwar wasu, ya kamata su zama masu yin irin rayuwar su ta kansu ba ta kwaikwayo ba ko karya sannan kuma su dage da yin aiki tukuru.

Copy the link below and Share with your Friends:

Download Our Official Android App on Google Playstore HERE
OR
Download from another source HERE



No comments:

Post a Comment