Rahama Sadau Ta Sha Da Kyar A Jami’ar Umaru Musa ‘Yar’Adua - NewsHausa NewsHausa: Rahama Sadau Ta Sha Da Kyar A Jami’ar Umaru Musa ‘Yar’Adua

Pages

LATEST POSTS

Sunday 17 December 2017

Rahama Sadau Ta Sha Da Kyar A Jami’ar Umaru Musa ‘Yar’Adua


Fittaciyar jarumar wasan  fina-finan Hausa wanda kuma ke fama da rikice-rikece a masana’antar a kwanakin nan, Rahama Sadau, ta sha da kyar a jami’ar Umaru Musa ‘Yar’Adua, dake Katsina bayan da wasu gungun daliban jami’ar suka yi kokarin murkushe ta a harabar makarantar da aka fi sani da ‘Students’ Centre’.

Rahotanni  sun shaida mana cewa shugabannin daliban jami’ar ne suka gayyaci jarumar domin su karramata a lokacin wani biki da suka shirya don tuna wa da ranar mata ta duniya.

Majiyarmu sun  bayyana mana cewa fitacciyar jarumar wadda tazo a makare a wurin taron bayan anyi nisa a ciki ta nemi wuri ta zauna ne a inda aka tanada domin ta kafin daga bisani a kira ta domin a bata shaidar karramawar da aka tanadar mata.

Tun farko dai rahotannin sun bayyana  cewa zuwan jaruma Rahama Sadau din ke da wuya sai kawai kallo ya koma mata yayin da wurin ya fara harmutsewa da lokacin da dliban jami’ar masoyan ta suka fara kokarin yin tozali da ita wasu kuma suna kokarin yin hotunan nan na dauka-da-kai watau (Selfie) a turance da jarumar.

Majiyoyin  sun  ci gaba da cewa kafin kace kala wurin ya ya mutse inda wasu daga cikin daliban suka rika kokarin afkawa ma jarumar da manufofi daban-daban.

Ganin haka ne ma yasa jami’an tsaron jami’ar da kuma sauran shugabannin daliban suka yi kokarin fita da jarumar da karfi wanda hakan kuma ya kara tayar da wata hatsaniyar.

Binciken mu dai ya tabbatar mana da cewa babu abun da ya samu jarumar inda aka yi nasarar fitar da ita lafiya.

A dayan bangaren kuma dukkan kokarin da mukayi don jin ta bakin shugabannin daliban da ma ita kan ta Rahamar bai yi nasara ba.

Sources: Arewa Dailypost

Copy the link below and Share with your Friends:

Download Our Official Android App on Google Playstore HERE
OR
Download from another source HERE



No comments:

Post a Comment