Na yanke hukunci kan takarar Buhari a 2019 — Aisha Buhari - NewsHausa NewsHausa: Na yanke hukunci kan takarar Buhari a 2019 — Aisha Buhari

Pages

LATEST POSTS

Wednesday 12 October 2016

Na yanke hukunci kan takarar Buhari a 2019 — Aisha Buhari

Mai dakin shugaban Najeriya, Aisha Buhari, ta ce, ta riga ta yanke hukunci kan ko mijinta zai sake tsayawa takara a 2019.
A wata kebantacciyar hira da ta yi da BBC, Aisha Buhari, ta kara da cewa shugaba Buharin ya yi watsi da wasu 'ya'yan jam'iyyar APC wadanda suka sha wahala da mijin nata a lokacin gangamin yakin zabe.
Hajiya Aisha, ta ce lamarin ya sa ana samun rabuwar kawuna tsakanin 'yan jam'iyyar.
A cewarta, "Mutane da yawa sun fara rarraba kawunan 'yan jam'iyyar APC, kuma hakan yana kawo mana damuwa da yawa yanzu. Saboda suna ganin su suka yi wahala amma ba sa koina yau".
Ta kara da cewa, "Wadanda ba su yi wahala ba; wadanda ko katin zabe ba su da shi su suka zauna a kan mutane suke yin komai da komai. Abin da nake guje musu (su manyan APC) shi ne boren da mutum miliyan 15 za su yi".
An tambayi Misis Buhari ko mai gidanta ya san da wannan korafi, sai ta ce "ko ya sani ko bai sani ba wadanda suka zabe shi sun sani. Babu kuma abin da zan gaya masa don yana kallon abin da ke faruwa".
Uwargidan shugaban na Najeriya ta ce Shugaba Buhari bai san akasarin mutanen da ya nada a mulki ba, tana mai cewa yawancin mutanen da ke tare da shi 'yan-ta-yi-dadi ne.
"Cikin wadanda ya zaba ya nada idan an tambaye shi 45 cikin 50 ba saninsu ya yi ba. Bai san su ba. Haka nake zato. Ni ma ban san su ba saboda na zauna da shi shekara 27," a cewar ta.
Wannan wani bangare ne na hirar da muka yi da ita, inda a ranar Litinin ta yi magana kan irin aikace-aikacen da ofishinta ke gudanarwa domin tallafawa mata masu karafin karfi da kuma 'yan gudun hijira a Arewa maso Gabas.
Aisha Buhari ta ce mai gidan na ta bai gaya mata matsayinsa kan sake tsayawa takara a shekarar 2019, tana mai cewa "amma ni na yanke hukunci".
Sai ku kasance tare da mu a shirinmu na safe ranar Juma'a domin jin hukuncin da ta yanke da ma cikakkiyar hirarmu da ita.


Copy the link below and Share with your Friends:

Download Our Official Android App on Google Playstore HERE
OR
Download from another source HERE



No comments:

Post a Comment