LATEST :Ana zaman dar-dar a Kaduna - NewsHausa NewsHausa: LATEST :Ana zaman dar-dar a Kaduna

Pages

LATEST POSTS

Sunday 16 October 2016

LATEST :Ana zaman dar-dar a Kaduna

Rahotanni daga jahar kaduna dake arewacin Najeriya na cewa al’umma na zaman dar-dar sakamakon wani rikici da ya barke a jiya asabar a yayin da wasu mambobi na ‘yan uwa musulmi ta ‘yan Shi'a ke kokarin sake gina makarantarsu.
Wasu matasa ne suka soma far ma ‘yan shian a lokacin da suke kokarin gyare gyare a makarantar, rikicin ya sa mutane tserewa zuwa gidajensu, yanzu haka ma mazauna yankin sun ki fitowa don gudanar da ayyukansu na yau da kullum don gudun abinda zai biyo baya kamar yadda wani sheddun ganin da ido ya tabbatar.
Rahotanni na cewa ‘yan shia biyu ne suka mutu yayin da wasu goma suka sami rauni.



Copy the link below and Share with your Friends:

Download Our Official Android App on Google Playstore HERE
OR
Download from another source HERE



No comments:

Post a Comment