labari da dumi duminsa :kakakin jam'iyar APC ta goyi bayan Aisha buhari - NewsHausa NewsHausa: labari da dumi duminsa :kakakin jam'iyar APC ta goyi bayan Aisha buhari

Pages

LATEST POSTS

Saturday 15 October 2016

labari da dumi duminsa :kakakin jam'iyar APC ta goyi bayan Aisha buhari

Kakakin jam’iyyar APC, Timi Frank, yace matar shugaba Buhari ta cancanci yabo saboda ta fadi ba wai abunda ke zuciyar yan jam’iyya kawai ba, amma harda yan Najeriya a hirar da tayi da BBC kwanan nan
– Frank yayi kira ga matan Najeriya dake siyasa da matayen sauran shugabanni a duniya da su yi koyi da Aisha Buhari
– Kakakin na APC yace matar Buhari ta bayyana abunda take ji cikin kyayyawan nufi don ci gaban Najeriya da yan Najeriya

Kakakin jam’iyyar APC Timi Frank yace Aisha Buhari tayi furucinta ne don son ganin ci gaban Najeriya da yan Najeriya
Mataimakin sakataren labarai na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) Timi Frank, yace furucin da matar shugaban kasa, Aisha Buhari tayi a wani hira da ba hukumar BBC Hausa dama, abune da yan jam’iyya dama ke ji a zuciyoyinsu.
A cikin hirar da akayi a ranar Juma’a 14 ga watan Oktoba, matar Buhari ta nuna rashin jin dadinta kan yadda take hakkin yan jam’iyya daga wadanda ta ce basu taka ko wani rawa ba a nasarar da mijinta yayi na zama shugaban kasa amma su ke jin dadin abun a yanzu.
Da yake maida martani ga hirar, a wata jawabi da yayi a ranar juma’a, Frank yace matar shugaban kasa, Aisha Buhari ta cancanci yabo saboda ta fadi abunda ke zuciyoyin yan jam’iyya dama yan Najeriya a hirar. Haridar Punch ta ruwaito.
Frank yayi kira ga matan Najeriya dake siyasa da matayen sauran shugabanni a duniya da suyi koyi da Aisha Buhari.
Sannan kakakin na APC ya gargadi masu adawa kan yi wa furucinta mummunan fassara.


Copy the link below and Share with your Friends:

Download Our Official Android App on Google Playstore HERE
OR
Download from another source HERE



No comments:

Post a Comment