AN KORI RAHAMA SADAU DAGA MASANA'ANTAR FIM
A yau ne Kungiyar masu shirya Fina-finan hausa mai suna (MOPPAN) ta kori jaruma Rahama Sadau daga harkar Fim kwata-kwata, sakamakon wata wakar bidiyo da ta yi da wani mawakin Turanci mai suna Classiq. Wakar da ta jawo cece-kuce wurin al'umma. Har ta kai ga wasu daga cikin jaruman masan'anatar ta Kannywood sun fito fili karara suna goyon bayan a hukunta ta bisa laifin da ta aikata.
A da zu ne dai kungiyar ta zartar da hukuncin karkashin jagorancin shugabannin kungiyar kamar yadda sakataren kungiyar Moppan Salisu Muhammad officer ya sanar. A cewar sa Rahama ta taka doka shi ya sa suka kore ta daga harkar fim kwata-kwata. Sannan yace akwai amincewar sauran kwamitocin da ke karkashin kungiyar ta Moppan kafin Su zartar da hukuncin.
KARIN BAYANI: Sai dai manzarta da masu lura da al'amurran yau da kullum na masana'antar ta Kannywood suna ganin wannan hukuncin dai dai yake da kwance igiyar goro. Wargajewa zai yi ba zai yi tasiri ba. Saboda In dai ba a manta ba a ranar 4th ga watan mayu na shekara da ta gabata 2015 an taba dakatar da jarumar daga harkar Fim na tsawon Wata shida. In da a wancan lokacin wasu daga cikin furodusoshi da daraktoci su kayi fatali da hukuncin sannan suka ci gaba da sanyata a fina-finansu. Kuma suka ci bulus.
A gefe guda wasu kuma suna ganin babu adalci kan dakatarwar da aka yi jarumar saboda akwai wadanda suka yi abinda ya fi na ta muni kuma hotunansu su ma sunyi yawo kamar wutar bazara. Amma aka zuba masu ido ba tare da an dauki mataki akan su ba.
Yanzu haka dai kura naci gaba da tashi a industiri dangane da korar da aka yi wa Rahama sadau Inda wasu suke ganin hukuncin da aka yanke mata ya yi dai. Wasu kuma suna ganin kwata-kwata ba ayi mata adalci ba.
Madogara: Kannywood Exclusive Instgram Page.

Copy the link below and Share with your Friends:
No comments:
Post a Comment