MEYASA AKA BAMBANTA NAMIJI DA MACE A WAJAN RABON GADO ? - NewsHausa NewsHausa: MEYASA AKA BAMBANTA NAMIJI DA MACE A WAJAN RABON GADO ?

Pages

LATEST POSTS

Wednesday, 5 October 2016

MEYASA AKA BAMBANTA NAMIJI DA MACE A WAJAN RABON GADO ?

MEYASA AKA BAMBANTA NAMIJI DA MACE A WAJAN RABON GADO ?
*Tambaya?*
Assalamu alaikum mallam menene hukuncin wanda ke kokarin ganin an baiwa mace kason da aka bawa namiji wajen rabon gado?
*Amsa* :
Wa'alaikum assalam,
Ya sabawa Allah, Hakan kuma zai iya fitar da Shi daga musulunci in har ya yi gangancin haka, saboda kokari ne na warware hukuncin da Allah ya zartar. Allah da kansa ya raba gado bai wakilta wani don ya raba ba, ya bawa kowa hakkinsa gwargwadon kusancinsa da mamaci da kuma masalahar da Allah ya duba, wacce ya fi kowa saninta. Daga cikin hikimomin da suka sanya shariar Musulunci ta bambanta tsakanin mace da namiji a rabon gado shi ne: kasancewar hidimar namiji ta fi ta mace, yawancin mace idan tana karama tana karkashin kulawar mahaifinta, idan kuma ta yi aure tana komawa cikin kulawar mijinta. Allah ya yi alkawarin wuta mai kuna ga duk Wanda ya sabawa ayoyin rabon gado a cikin suratun Nisa'i aya:14, kamar yadda ya yi alkawarin Aljanna mai koramu ga wanda ya bi rabon da ya yi a cikin aya ta:13 a waccar Surat. Duk Wanda ya kiyaye dokokin Allah tabbas zai kiyaye shi, Wanda ya sabawa Allah, to yana nan a madakata, kuma mabuwayi ne mai tsananin karfi kamar yadda ayoyin Alqur'ani masu yawa suka tabbatar.
Allah ne mafi sani.
05/10/2016
*Dr. Jamilu Zarewa*


Copy the link below and Share with your Friends:

Download Our Official Android App on Google Playstore HERE
OR
Download from another source HERE



No comments:

Post a Comment