Sanata Rabiu Musa Kwankwaso
Tsohon Gwamnan Kano, Rabiu Musa Kwankwaso ya zargi Shugaban kasa Muhammadu Buhari da hannu dumu dumu wajen cire halastacen zababben Shugaban APC na jihar Kano Umar Haruna Doguwa. A cewar Kwankwaso, Buhari ne ke kara balabalawa wutar rikicin APC a Kano man fetur.
A lokacin da yake yiwa manema labarai jawabi a jihar Kano ranar Asabar, Shugaban ma’aikatan tsohon Gwamnan Kano, yace, Shugaban kasa ne da kansa ya bayar da umarnin a cire Shugaban APC na jihar Kano tsagin Kwankwasiyya, wanda kuma shi ne halastaccen shugaba.
Sannan yayi Allah wadai da cire Umar Doguwa daga mukaminsa, yace wannan yin karan-tsaye ne ga dokokin demokaradiyya tare da nuna mulkin kama-karya da dauki dora, yace dole duk mai kishin demokaradiyya yayi tur da abinda aka yi a jihar Kano.
Kwamared Abdulsalam yace, wannan abin Allah wadai, ba wasu bane suka kitsa shi sai su Sha’aban Ibrahim Sharada wanda yake zaman mataimaki na musamman ga Shugaban kasa kan kafafen yada labarai da kuma, Hafiz Kawu wanda shima ma’aikaci ne ga Shugaban kasa, sai kuma Bashir Ibrahimwani aminin shugaban kasa.
“Mun samu tabbacin cewar, Shugaban kasa ne da kansa ya bayarda umarnin a cire halastaccen zababben Shugaban APC na jihar Kano Umar Haruna Doguwa, ta hannun Sha’aban Sharada, da Hafizu Kawu wanda mataimaki na musamman ne ga mataimakin shugaban kasa, da kuma Bashir Ibrahim Gwammaja”
“Wadannan mutane, tare da wasu tsirarun mutane a fadar Shugaban kasa, su ne suka jagoranci Sakataren jam’iyyar APC na kasa Mai Mala Buni wannan mummunan karan-tsaye da aka yiwa demokaradiyya,inda suka cire halastaccen Shugaba, inda ska maye gurbinsa da wani dan gani-kashenin Abdullahi Umar Ganduje”
“Dan haka,a matsayinmu na halastattun ‘yan jam’iyyar APC a jihar Kano,muna Allah wadarai tare da yin tur da wannan mataki da aka dauka na yin karan tsaye ga tanade tanaden demokaradiyya, akakarya dukkan tsarin mulkin jam’iyya, aka cire halastaccen shugaban jam’iyyar da aka zaba, sannan aka kakabawa mutane wani mutum na daban”
“Babu wata ganawa da aka yi a majalisar koli ta kwamitin amintattu na jam’iyyar APC ko majalisar zartarwa jam’iyyar APC ta kasa balle a dauki wannan mataki, wannan abin tur ne, domin abinda suka yi ya sabawa sashi na 21 na kundin tsarin mulkin jam’iyyar APC”
“A sakamakon faruwar wannan al’amari, muna masu nuna rashin amincewarmu, tare da kin gamsuwa da wannan mataki da akadauka na cire halastaccen Shugaban jam’iyyar APC na jihar Kano, dan haka, zamu cigaba da ganin wannan abu da akai a matsayin karantsaye ga dokokin demokaradiyya”
“Mu a zatonmu a yanzu, an wuce lokacin da za’a dinga dorawa mutane abinda ba shi ne zabinsu ba, wannan sam bai dace da siyasar wannan zamanin ba, da mutane suka samu wayewa da sanin abinda suke yi”
“Dan haka, daga karshe, muna yin kira da babbar murya ga uwar jam’iyyar APC ta kasa, da ta dauki matakin dawo da tsohon Shugaban jam’iyyar na jihar KAno wanda aka cire ba bisa ka’ida ba, idan kuwa ba haka ba, abinda zai faru da jam’iyyar a nan gaba, ba zai haifar mata da da mai ido ba” A cewarsa.
Copy the link below and Share with your Friends:
No comments:
Post a Comment