Kano Muhammadu Sanusi ya goyi bayan 'yan fim - NewsHausa NewsHausa: Kano Muhammadu Sanusi ya goyi bayan 'yan fim

Pages

LATEST POSTS

Thursday 21 December 2017

Kano Muhammadu Sanusi ya goyi bayan 'yan fim

Fina-finai a Najeriya na taka muhimmiyar rawa wajen hada kan 'yan kasa tare kuma da tabbatar da raya al'adun al'ummar mu inji Sarkin Kano, Alhaji Muhammadu Sanusi Lamido na biyu.

Sarkin na Kano dai yayi wannan bayanin ne a yayin da wasu fitattun 'yan fim din daga masana'antar shirya fim din Hausa na Kannywood da kuma na fina-finan 'yan kudancin Najeriya watau Nollywood suka kai masa ziyara a fadar sa.

NAIJ.com dai ta samu haka zalika cewa Sarki Sanusi ya kuma bayyana cewar ko shakka babu haduwar jaruman fina-finan daga masana'antun kudu da Arewa da cewar abu ne mai kyau da zai dada kara hadin kan al'ummar kasar musamman ma a yanzu da siyasa ta raba kawunan mutane da dama.

Copy the link below and Share with your Friends:

Download Our Official Android App on Google Playstore HERE
OR
Download from another source HERE



No comments:

Post a Comment