A bisa labarin da jaridar Vanguard ta fitar, shugaban yace ya kama tare da garkame masu yi aikata barna a kasar a zamanin da yake shugabancin mulkin soja.
Buhari ya kara da cewa a bangaren yaki da cin hanci da rashawa, mawuwaci ne a gamsar da yan Nijeriya.
Shugaba Buhari yayi wannan bayani ne garin Abidjan babban birnin kasar Cote D'ivoire yayin da yake ganawa da yan Nijeriya mazaunin kasar lokacin da ya ziyarci kasar domin halartar taron gamayyar majalisar hadakar kasashen Afrika da ta nahiyar turai.
Buhari yayi ikirari cewa a lokacin kuruciyar shi yayin da yake soja ya kama wasu tsoffin ministoci da gwamnoni inda har ma aka kulle su a gidan kaso ta kirikiri har lokacin da suka shirya nuna gaskiya game da laifin da ake zargin su da yi.
Yana mai cewa " yanzu da muka dawo karagar mulki, kowa na ikirari cewa su masu gaskiya ne har sai lokacin da aka kama su da laifi. Hakazalika yan Nijeriya na cewa muna tafiyar hawainiya game da game da kama su. yanzu ya zamu yi da haka? sai dai mutum ya iya bakin kokarin shi amma ina mai cewa babu yanda za'a gamsar da mutanen mu dake gida Nijeriya.
Shugaban yace barnar da ake yi yanzu ya sha bambam da wanda ake yi zamanin da yake shugabancin mulkin soja amma zai cigaba da kokartawa domin shi ya sa kanshi kuma zayi iya bakin kokarinshi wajen sauya yadda alamuran ke tafiya.
Sources:jarida vanguard
Copy the link below and Share with your Friends:
No comments:
Post a Comment