Daga Aliyu Ahmad
Masu garkuwa sun sako jarumin finafinan Hausan nan Al-Amin Buhari bayan an biya Naira dubu 500.
A yayin jin ta bakin Furodusan finanan Hausan nan, Usman Mu'azu ya tabbatarwa da RARIYA cewa a halin yanzu jarumin yana Abuja, kuma ana sa ran gobe Laraba zai dawo Jos.
Masu garkuwa sun yi garkuwa da jarumin ne a kusa da garin Keffi bayan ya taso daga Abuja zuwa Jos a ranar Lahadin da ta gabata.
Copy the link below and Share with your Friends:
No comments:
Post a Comment