DA DUMIDUMINSA Wani Dan Majalisa Ya Sake Rasuwa - NewsHausa NewsHausa: DA DUMIDUMINSA Wani Dan Majalisa Ya Sake Rasuwa

Pages

LATEST POSTS

Friday 30 March 2018

DA DUMIDUMINSA Wani Dan Majalisa Ya Sake Rasuwa



Dan majalisar tarayya daga jihar Kogi, mai wakiltar Lokoja/Kogi/Koton Karfe, Umar Buba Jibril ya rasu yana mai shekaru 57.

Majiya daga iyalan mamacin ta bayyana cewa marigayin ya rasu ne a Abuja sakamakon rashin lafiya da ya yi fama da ita.

Rahotanni sun nuna mamacin ya jima yana fama da rashin lafiya, wanda hakan ya sanya ya dauki kusan shekara guda bai halarci zama a majalisa ba. Inda aka rawaito cewa rabon da ya halarci zaman majalisa tun lokacin da shugaba Buhari ya gabatar da kasafin kudi.

I dan ba a mance ba a makonni kusan uku da suka gabata Sanata Ali Wakili daga jihar Bauchi ya rasu.

Copy the link below and Share with your Friends:

Download Our Official Android App on Google Playstore HERE
OR
Download from another source HERE



No comments:

Post a Comment