Jarumar ta bayyana hakan ne a shafinta na twitter a yayin da take maida martani ga wata ma’abociya shafin da tayi ikirarin cewa fim din rariya ka iya bisa abinda ta gani sanya ma iyaye rashin kwarin gwuiwar barin yaransu mata zuwa makarantun gaba da sakandire don fadada karatun su.
Sai dai jarumar wacce itace ta shirya wannan shiri ta maida martani da cewar fim din rariya anyi shi ne don ya haska ma iyaye akan su kasance masu sanya ido sosai a kan yadda yaransu ke rayuwa a makarantu don su gargade su akan su sani gami da kare mutuncin kansu, kar su biyewa mutanen da ka bige da yaudarar su da abin dunya don jefa su cikin wata rayuwa ta daban.
Film din Rariya na cikin fina-finan da akayi ikirarin sun kayatar sosai a fina-finan da suka fita a cikin shekarar data gabata, duba da yanayin yadda aka yi shi bisa wasu abubuwa dake faruwa a cikin al’umma.
Shin jama’a kun gamsu da wannan batu na jaruma rahama sadau?
Copy the link below and Share with your Friends:
No comments:
Post a Comment