Sarkin Damagaram, Mai Martaba Alhaji Abubakar Sanda, ya sanar da rage farashin sadakin mata A masarautar sa ta Damagaram a jamhuriyyar Nijar
Sarkin ya sanar da hakan a lokacin da ya halarci wani taro na masu ruwa da tsaki,
wanda ya hada da 'yan kasuwa da kuma kungiyoyin mata a jihar ta Damagaram,
Sarkin ya ce masarautar ta dauki wannan kudurin ne bayan jama'ar garin sun kai masa kukansu akan a sama musu sauki akan al'amuran da suka shafi aure da bikin suna da kuma wasu manyan bidi'oi a yankin jihar. Wanda a cewar sa hakan ya sanya maza basu iya aure sosai kuma mata suna ta karuwa babu mazaje, Sarkin yace wannan ragin zai rage yawan yan mata marasa aure
A yanzu haka dai, masarautar ta garin Damagaram ta rage kudin sadakin aure daga jaka 50 zuwa jaka 20, sannan kuma masarautar ta hana daukan amarya a cikin jerin gwanon motoci, sannan an rage kayan gara, daga karshe kuma an hana yin ankon biki kwata-kwata a jihar. Duk dai da nufin samar da sauki cikin sha'anin aure,
Copy the link below and Share with your Friends:
No comments:
Post a Comment