Manchester City da Manchester United Sun Shiga Cikin Masu Zawarcin Neymar - NewsHausa NewsHausa: Manchester City da Manchester United Sun Shiga Cikin Masu Zawarcin Neymar

Pages

LATEST POSTS

Monday 12 March 2018

Manchester City da Manchester United Sun Shiga Cikin Masu Zawarcin Neymar



Wani shafin harkar tamaula dake yanar gizo, Diario Gol (www.diariogol.com) ya bayar da labarin cewa kungiyoyin kwalon kafa biyu dake bugawa a wasannin Firimiya Lig na Ingila a birnin Manchester, watau City da United, sun shiga cikin jerin masu zawarcin dan wasan Brazil da kuma kungiyar PSG ta Faransa, Neymar Jr.

Ana rade-radin cewa Neymar ba ya jin dadin zamansa a kungiyar PSG, kuma yana kwadayin a sayar da shi ma wata kungiyar bayan shekara daya kawai a Faransa.

Har yanzu yana kwadayin komawa kungiyar Real Madrid mai bugawa a gasar La Liga, amma rahoton na Diario Gol yace Neymar ba zai ki komawa Manchester City ba, idan har aka kasa cimma daidaito kan komawarsa zuwa Real Madrid.




Copy the link below and Share with your Friends:

Download Our Official Android App on Google Playstore HERE
OR
Download from another source HERE



No comments:

Post a Comment