Babban Shehin yan Shi’a ya Kwance Masu Zani a kasuwa - NewsHausa NewsHausa: Babban Shehin yan Shi’a ya Kwance Masu Zani a kasuwa

Pages

LATEST POSTS

Thursday 8 March 2018

Babban Shehin yan Shi’a ya Kwance Masu Zani a kasuwa

Rahotanni sun kawo cewa babban Shehin Musulmai mabiya Shi’a, Kamal Al Haidari ya yayewa mabiyansa zani a kasuwa, inda ya bayyana cewa mafi akasarin hadisansu Kirista, Majusawa da Yahudawa ne suka rawaito su.

Shugaban kungiyar na asali, ya furta wannan kalamin a yayin wani shirin talabiji, inda ya ce :

"Mafi akasarin hadisan mabiya Shi'a Rafidha, Kirista, Majusawa da Yahudawa suka rawaito su, a ciki har da littafin tafsiri na AL Qomi wanda ya kasance daya daga cikin sanannun litattafai.


"Wadannan litattafan na kunshe da karyace-karyace, kwaskwarima,kazafi da aika-aika marasa misaltuwa, duk da Malam Al Khoei ya nemi tsaftace su.


"Kowa ya san da haka, amma wasu jahilan malamai masu sanye da bakeken alkyabbobi ke ci gaba da rufe ido don yin amfani da su a wajen batar da jama'a".

Copy the link below and Share with your Friends:

Download Our Official Android App on Google Playstore HERE
OR
Download from another source HERE



No comments:

Post a Comment