“Ko ina Kano aka yi bad’alar gidan gwamnati sai dai mu yi Allah ya isa”!!! Malam Aminu Ibrahim
Malam Daurawa yayi wannan jawabin ne a ranar Juma’a, 16-3-2018 a wajen karatun littafin “Adabul Mufrad” da yake gabatarwa duk sati a majalisin Ansarissunah na Marigayi Sheikh Abubakar Hussein (Albany) da ke Fagge, jihar Kano. Na yi qoqarin tsakuro jawabin da malam yayi akan surutu da kakaci da jama’a suke yi game da shirun da malam yayi akan “rashin kunya da fitsara” da Fatima Abdullahi Ganduje ta yi a wajen bikinta.
Malam yace: “a tafiyar da muka yi a satin nan, na samu saqo sama da 2000. Da hotuna da bidiyo. Aka yi ta yi min waya ana cewa “malam ana ta6argaza a Kano, ana raye-raye da kad’e-kad’e. Bayan na dawo, y’an jarida (da na Fesbuk, da na Whatsapp, da na rediyo, da na talabijin) suka cika a Hizbah suna jirana. Sai wani malami yayi min text, yace idan ka ga text dinnan ka kira ni. Na kira shi. Yace an ce ka tara y’an jarida a Hizbah za ka zuba, to kar [ka sake] ka zuba. Sai ya kashe wayarsa. Sai wani d’an jarida ma ya kirani, yace malam gamu duk an tara mu ana jiran kai so, to don Allah shawarar da zan bayar, kar kayi Magana akan abun. Amma ba dole ka d’au shawarata ba. Duk abinda ka ga dama kayi. Amma don Allah kar ka yi Magana. Na ce ai ni yanzu kun saka ni a tsaka mai wuya. Idan ban yi magana ba ace anyi laifi anyi shiru. Yanzu wanne zan d’auka? In je in yi cashiyata in more? Ko in yi shiru? Wanne ya fi?
Idan na yi shiru, wad’anda suka saba in an yi abu ina magana, to za su ce to me ya sa malam yayi shiru. Wancan malamin kuma malamina ne, na yi karatu a agurinsa, yana cikin malaman da duk Kano ana girmama su. Shi kuma yace kar nayi magana, yanzu ina zan sa kaina! Don haka sai na zagaye na qi shiga Hizbar. Y’an jarida suka yi ta nema na. Na ce musu ina makaranta. Sai ga su yuuuu. Ni nake gudu suna bina [suna cewa] ‘akaramakallahu an yi ta6argaza, an yi 6arna, an yi shegantaka, an yi tsalle-tsalle, an yi raye-raye, an kad’a d’uwawu, innalillahi wa inna ilaihirrajiun! Addini ya mutu a Kano. Mu talakawa da muke sa6o ku daina hana mu. Tunda ba kwa hana manya . . . . . Wani kuma yace akaramakallahu da kana bud’e wuta, yanzu kuma ka daina bud’e wuta. Wani kuma yace abinda ya sa malam ya qi magana, malam yana kare kujerarsa da muqaminsa ne. Kar yace yar gwamna ta yi tabargaza gwamna ya cire shi. To ni da hizbah wa yake kare wani? Kujerar Hizbah har ta na da wani dad’in da za ka kare ta? To jiya ma sai da aka kaini qara kotu. Qungiyar kiristocin Kano sun dauki lauyoyi sama da goma sha, aka ce wai NA HANA MUTANE SU YI RIDDA A KANO!!!
Ka fito kace an yi ta6argaza a bune mai sauqi. Amma abubuwa dole ana tafiya ana lissafa su. In dai yanzu abinda mutane suke so za ka yi, to wallahi baza kayi komai ba. Duk abinda muke yi, yardarm Allah muke nema. Lokacin yakamata ayi magana za ayi. Lokacin da yakamata ayi shiru za ayi. Mutane so suke mu ringa yin abinda zai burge su, ba wai don Allah ba. Kamata yayi mutum yayi abinda ya dace. Da me zaginka, da mai yabonka, kowa yaje yayi abinda ya ga dama, irin tarbiyyar gidansu kenan. Duk wanda Allah ya bashi qarfin mulki, to ba kowane mai qarfi ba ne a qasa zai iya tunkararsa. Mu Hizbah kwamiti ne qwaya d’aya acikin kwamitocin gwamnati. To ta ya ya za ka kama fad’a da gwamnati? Sai dai ka yi mata nasiha! SAI DAI [MATSALAR] SU YAN SIYASA SUN FI JIN NASIHA A LOKACIN ZABE (shebi you understand?). BA SA JIN ALLAH YA CE ANNABI YA CE. SUN FI JIN TSORON RANAR ZABE. RANAR DA TALAKA ZAI RAMA. Ina cikin gwamnatin, aka zo aka ce za ayi fim village a Kano, gwamnatin na da ra’ayi, na fito nace ban yarda ba! Har daga fadar shugaban qasa sai da aka kira ni. A ka zo aka yi maganar rage shekarun auren y’a mace, duk da na san gwamnatin na da hannu aciki, amma nace ban yarda ba.
A baya mun yi makamanciyar wannan maganar akan Masallacin Idi! Muka kira taron y’an jaridu. Muka ce mu a matsayinmu na malamai da suke cikin wannan gwamnatin (Zakkah, Hizbah, Shari’a) BA MU YARDA GWAMNATI TA MAIDA MASALLACIN IDI YA KOMA KASUWA BA. Muka rubuta arubuce, duk muka sa hannu, muka kaiwa gwamnati muka ce muna bada shawara kada ta kuskura ta ringa yanka massalaci ana siyarwa. Duk da mun yi abinda kuke so d’in, amma bai yi amfani ba. Kuma kowa yana kallo, ba wanda yace qala. Daga baya ma sai aka zo aka ce an bawa malamai fili d’ai-d’ai [hahhahahah]! Muka je muka kewaye masallacin, y’an jarida suka ringa cewa muna zanga-zanga [kun san an yi haka?]. Mu kace don Allah a qara inganta masallacin, a gyara shi, a sa masa tsaro, a qara fito da darajar Kano, amma [gwamnati] ta yi watsi da mu!
WANNAN BIKIN NA FITSARA, a halin yanzu, a koi’na ana yin shi. Gidajen da ake yi [a Kano] sun fi 100. Mun yi mun yi adaina, da mun bi ta can, sai azo mana da wata doka, ko mutum yayi rijista da da Fed govt. Wani gurin idan ka je ba zai shigu ba. Za ka tarar da sojoji da bindigogi. SU KUMA YAN HIZBAH BA YAN BOKO HARAM BANE! BALLE SU SHIGA GURI SU KWASHI YAN MATA KAMAR YADDA AKA KWASHI MATAN DAPCHI! Wani gurin za su je suga ana badala, amma ga sojoji a bakin gate, sai ince ku taho, ALLAH YA ISA! Yanzu ko ance ana badala a gidan gwamnati, ya d’an Hizbah zai shiga gidan gwamnati ya kamo wani? Gidan gwamnati fa! ‘Dan Hizbah ya je ya ture SOJA, DA DAN SANDA, DA DAN SIKYURITI, YA KAMA YAR GWAMNA, YA KAMA MATAR GWAMNA, YA KAMA MATAR WAYE . . . . . HABA!!! Ko da ina nan aka yi wannan sai dai mu yi Allah ya isa! Abun ya fi qarfinmu. Dokar da ta kafa abun [Hizbah] ba za ta iya ba.
Akwai gwamnan Sakkwato, ana bikin y’arsa, yan Hizbar Sakkwato suka yi kabbara, suka ce Allahu Akbar, aje a tashi bikin, suka kai farmaki, sai gwamnan yace ya rushe Hizbar. Ba wanda yayi Magana [hahhahhhhah]. Sai ni na tashi na je na same shi, nace your excellency, ka yi haquri ka dawo da Hizbah, yace to malam ga abubuwa [kaza da kaza], nace yi haquri, yanzu ya bani aikin dawo da Hizbah a Sakkwato. Na je na samu gwamnan Katsina, nace don Allah ka kafa Hizbah, za ta yi muku amfani, yace ance in sun kama mutum, sai sun bud’a bakinsa sun shinshina sun ji wai ko ya sha giya. Na ce ba haka bane. Mun kafa makaranta a Kano wacce za ta ringa ba da ilimi. Ba za aringa bin mutum da gudu ba. Ko yanzu in ana biki, in aka kawo min rahoto, cewa nake kar ku je. Idan an fara kar ku je. Idan an gama kar ku je. Ku kawo min sunan mai gidan da adireshinsa. Idan an fara, ka tafi da gudu, akwai mata, akwai masu goyo, akwai yara qanana, da ance ga y’an Hizbah nan, sai a fara guje-guje, sai wani ya karye, wani ya ji ciwo, sai kuma a zo ace y’an Hizbah tsinannu! Subhanakallahumma wa bi hamdik . . . .
Tsokaci: Wad’annan duk bayanan Malam Aminu Ibrahim Daurawa ne. Babu kalma ta ko d’aya. Kuma malam zai yi magana akan bikin nan. Wannan kamar wata y’ar shimfida ce. Domin kawai magana ce ta shigo. Domin bi sa al’ada, malam ya fi yin cikakken jawabi wajen amsa tambayoyi. Kuma akwai sauran bayanai masu faida wanda ban kawo su ba. Saboda yanayin lokacina. Ga ma son kashe qishirwarsa akan cikakken bayanin, sai ya nemi karatun da kansa. In sha Allahu zan zo na yi sharhin wasu kalmomi daga kalaman malam.
Dukku Mai son Sauke audio sai ya shiga cikin Wannan link din
👇🏽👇🏽👇🏽
Download Audio here
Ayi Sauraro da Karantawa lafiya
Copy the link below and Share with your Friends:
No comments:
Post a Comment