Tsara labari: Auwal M Sarki
Furodusa: Muhammadu Mia
Bada umarni: Ali Gumzak
Kamfani: Mia Enterprises
Jarumai: Aminu Sharif Momo, Fati Shu’uma, Sadiya Kabala, Hadiza Muh’d, Malam Inuwa, Nasir Naba, Malam Haruna, Baba Saugiji, Sayyid Ali Muh’d da Rahma MK .
Sharhi: Saddika Habib Abba
A farkon fim din an nuna Yahaya(Al’amin Buhari) yana korar ‘yarsa Fa’iza (Sadiya Kabala) daga gidansa sakamakon dakko masa abin kunya da ta yi a ranar daurin aurenta aka zo da hoton bidiyo na lalata da ta yi hakan tasa ya yi fushin zuciya yaki saurarar duk wasu masu bashi hakuri hatta mahaifiyar Fa’izar Talatu(Hadiza Muh’d)
A lokacin Fa’iza ta saka kafa ta shiga duniya sakamon korarta da mahaifinta ya yi, ta fara da shiga garin Zariya gurin wata shaharrariyar karuwa Zee Ta Kowa(Fati Shu’uma) domin ta kara bunkasa kwarewarta a bariki zaman su da Zee Ta Kowa yaki da di sakamakon ita Fa’iza tsayyayiyar yarinya ce kuma mara kunya tana ji da kanta domin babu wanda ya isa ya lankwasa ta kuma ta yi masa biyyaya saboda ita asali ba karuwa bace kaddarace ta fito da ita. ita kuma Zee Ta Kowa tunda shugaba ce a wajen dole kowa ya yi mata biyyaya sakamakon kin wannan biyyaya da Fa’iza ta yi mata ta sanya suka rabu baran baran Fa’iza ta kama gabanta daga nan ta tafi ta hadu da wani shaharran dan duniya mai suna Dan Agulla(Aminu Sharif Momo) suka ta fi suka bar Zariya suka wuce Kaduna suka fara sheka ayarsu, Dan Agulla direban mota ne yana da uban gida wanda suke gudanarda harkokinsu tare mai suna Alh. Maina wanda shi wannan Alhajin shine ya fara lalata rayuwar Fa’iza a baya sakamakon sunje gurinsa ita da kawarta domin ya basu hayar hall din bikin Fa’izar da za’ayi domin sun gayyaci kawayensu basa son suji kunya shi wannan Alhaji Maina ya yanka musu kudi mai tsada wanda za su kasa biya, ta hanyar daya samu dama ya bullowa da Fa’iza bukatarsa kenan ta fasinkanci da sharadin cewar idan ta amince zai bata hall din kyauta Fa’iza ta ki Amincewa a lokacin wata kwararriyar karuwa kawar Fa’iza mai suna Bintu (Hafsat Idris) ta tursa sa Fa’iza ta ribace ta har ta amincewa Alh.Maina domin gudun kada suji kunya shine hotan bidiyon da aka kawo gidansu ranar daurin auren amma kafin haka Fa’iza kamilalliyar yarinya ce, bayan Fa’iza sun hadu da Dan Agulla ranar da ta fara ganin Alh. Maina a matsayin shine uban gidan Dan Agulla abinda ya faru a baya ta fara tunawa irin ta’asar da ya yi mata a baya.
A bangaren gidansu Fa’iza kuma mahaifinta ya yi nadamar korar Fa’iza daga gida da ya yi kuma mahaifiyarta ta dame shi da kuka da damuwa sannan ga mahaifinsa ya yi fushi da shi kuma ya kafa masa sharadin cewar lallai duk in da jikarsa ta ke yaje ya nemo ta hakan tasa mahaifin Fa’iza ya bazama yawon nemanta gari gari duk inda yaje baya samunta sakamakon tana can Kaduna tare da Dan Agulla suna sheka ayarsu domin Fa’iza ta sha alwashin tunda mahaifinta bai ga kaddarar data fadamata ba ya kore ta to ita kuma sai ta dakko masa abun kunyar da ya fi na da wato dan shege.
A bangaren kawar Fa’iza Bintu kuma sun kulle da Alh.Maina domin dama tun tuni ita karuwace bakin cikinta ma shine ya yi sanadin rasuwar mahaifiyarta a karshe har suka sakawa juna cutar kanjamau kowannensu ya gane kuskurensa, ita kuma Fa’iza burinta ya cika ta yi ciki ta haihu a lokacin ta koma gida ta kaiwa mahaifinta dan shege hankalinsa ya yi matukar ta shi kuma ya yi nadamar korar Fa’iza da ya yi a baya itama Fa’izar ta yi nadamar abinda ta aikata.
Abubuwan Birgewa:
1- Jaruman sun yi kokari sosai gurin isar da sakon musamman Fa’iza da Dan Agulla.
2- An yi amfani da kayan aiki masu kyau kamar camera ta daukar hoto da kuma Abin daukar sauti da gida je da suka dace da labarin.
3- Anyi amfani da salo na harshe masu kayatarwa sannan da kwarewa gurin furtasu wato (dialogue).
Kurakurai:
1- Yakamata a nunawa mai kallo mijin da Fa’iza zata aura aka fasa.
2- Yakamata a nuna makomar Dan Agulla mara kyau saboda irin barnar da ya tata saboda darasi.
3- An nuna Fa’iza kamillaliyar yarinyace a farkon fim din mai kuma ya hada su kawance da Bintu karuwa? kuma har a gidansu aka bari duk da sun san ‘yarsu mai tarbiyyace?
4- Farkon haduwar Fa’iza da Dan Agulla lokacin da ya dauketa suka tafi tare lokacin dare ne daga nan suka sauka a garin da za su je da safe maikallo bai ga Fa’iza da jakar kaya ba kuma a wannan karamin lokacin ba’aga sun tsaya sun siya ba amma sai ga shi da suka sauka a garin da za su je da safe an ga Fa’iza ta canja kaya shin a ina ta samu?
5- Duk rashin mutuncin mutum mahaifiya ba wasa bace babu yanda za’ayi mutum ya shigo gida ya tarar mahaifiyarsa ana kurma ihun ta mutu amma ya nuna halin ko in kula kuma yana cikin hayyacinsa kamar yanda Bintu ta yi a fim din sam hakan a gaske abune wanda bazai faru ba.
6- Shin babban Mutum kamar Alh.Maina ba shida iyali ne? yakamata ace an rarrabewa mai kallo ko da a baki ne.
7- A lokacin da mahaifin Fa’iza yana nemanta har suka hadu a wani waje shi da ita ta saka nikaf ta rufe fuskarta kallon da ya yi mata ido cikin ido babu yanda za’ayi ace bai gane ta ba.
8- A gurinda Fa’iza taje ta sami Bintu a yashe tana jinya domin ta mayar mata da martani sai aka ji Bintu ta nunawa Fa’iza cewar tasan jiya ta dawo shin ta yaya Bintu ta san cewar Fa’iza ta dawo jiya? ita da take a kango a yashe tana jinya?
9- Acikin fim din yakamata idan an dauki tsahon wani lokaci wani abun ya faru a rubuta mai kallo ya gani bayan kazaa saboda tabbacin cewar abun zai faru a wannan tsahon lokacin misali kamar daukar cikin Fa’iza da haihuwarta an nuna su a lokaci kan kani.
10- Yakamata anunawa mai kallo sanadin daya sa asirin su Fa’iza ya tonu har aka kawo hoton bidiyo dinta ranar daurin aurenta sannan a nuna wanene ya kawo.
Karkarewa:
Fim din ya yi kyau sannan akwai darasi amma wasu kalamai da akayi amfani da su sun yi tsauri dayawa ya kamata a sakaya yanda kowa zai iya kalla hatta kananan yara saboda an bude abubuwa ko don saboda tarbiyyar kananan yara.
Copy the link below and Share with your Friends:
No comments:
Post a Comment