Shahararren malamnin nan kuma daya daga cikin jagororin darikar Tijjaniya dake garin Zaria, Sheik Tijjani Abdulkadir Zaria, ya bayyana cewa za a gudanar da Mauludin Sheik Ibrahim Nyass ne a garin Kaduna sabanin yadda wasu ke yada jita-jitar cewa za a gudanar da Mauludin ne a babban birnin tarayya Abuja.
Shehin Malamin ya yi kira da mabiya Darikar Tijjaniyya da su yi watsi da jita-jitar da ake ta yadawa na cewa za a gudanar da Mauludin ne a Abuja.
Ya ce duk wanda ya samo wannan rahoto, ya samo sa ne ta barauniyar hanya, wanda ba shi da asali. Domin tun farko an tsara ne cewa za a yi Mauludin a Kaduna.
Shehin ya ce wasu mutane ne daga cikin su suke nema su yi amfani da wata dama da suke da ita domin kawo ruduni game da Mauludin.
Ya ce Abuja ba ta nemi a bata karbar bakoncin Mauludin ba, amma jihar Kaduna ta nema, daga bisani kuma kwamitin kungiyar suka amince a gudanar a Kaduna. Ya kuma kara da cewa duk wanda ya ce Abuja za a gudanar, ya kawo masa takardar da ta tabbatar da cewa a Abuja za a gudanar da Mauludin.
Ya kuma kara da cewa kungiyar dake gudanar da Mauludin wato Maj'maul Ahbabul Sheik tana da rijistarta, kuma ita ta bayyana jihar Kaduna a matsayin wurin da za a gudanar da Mauludin, don haka bai ga amfanin wasu da ba su da hurumi a kungiyar ba su kawo cikas a tafiyar.
Sheik Tijjani Zaria ya kara da cewa ko muryar wa aka ji ya bayyana cewa ba a Kaduna za a gudanar ba, kada a yarda da shi.
Za a gudanr da Mauludin na Sheik Nyass ne wanda aka saba gudanarwa a duk shekara a ranar 14 ga watan Afrilu, 2018 a dandalin Murtala Square dake garin Kaduna.
Copy the link below and Share with your Friends:
No comments:
Post a Comment