Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa, shugaba Buhari ya bayyana hakan ne a jihar Katsina, yayin biki na rufe taron gasar karatun Al-Qur'ani ta kasa da aka gudanar karo na 32 a ranar Asabar din da ta gabata.
Shugaba Buhari yake cewa, ko shakka babu Al-Qur'ani shine babban kundin tsari da ya kunshi duk wani tafarki na rayuwar bil Adama. Kuma littafin Mai Girma ya koyar damu yadda zamu yi gaskiya da kuma adalci a duk mu'amalan mu da ya hadar har wadanda ba musulmai ba.
Ya ci gaba da cewa, "tarihin rayuwar Manzo kuma Annabin mu Muhammadu Sallalahu Alaihi Wassalama ya bayyana cewa, akwai wani lokaci da aka tsananta wa Musulmai, inda suka koma wata Daula ta kafirai a kasar Habasha kuma suka zauna lafiya tare da aminci".
karamin ministan sufuri na jiragen sama, Hadi Sirika, shine ya wakilci shugaba Buhari a wannan taro.
Ya kara da cewa, ya kamata mu riki Al-Qur'ani a matsayin madubin haskaka rayuwar mu ba abin kawata gidajen mu ba.
Copy the link below and Share with your Friends:
No comments:
Post a Comment