Rauni zai hana Neymar Da Silva karawa da Ronaldo na Madrid - NewsHausa NewsHausa: Rauni zai hana Neymar Da Silva karawa da Ronaldo na Madrid

Pages

LATEST POSTS

Tuesday 27 February 2018

Rauni zai hana Neymar Da Silva karawa da Ronaldo na Madrid

Ga alama gwarzon dan wasan PSG, wato Neymar De Silva ba zai samu damar buga wasan da kungiyarsa za ta yi da Real Madrid ba a gasar cin kofin zakarun Turai, matakin kungiyoyi 16 zagaye na biyu saboda raunin da ya samu a kafarsa kamar yadda binciken likitoci ya tabbatar.

Neyma mai shekaru 26 kuma dan asalin kasar Brazil ya gamu da raunin ne a fafatawar da PSG ta doke Marseille da 3-0 a ranar Lahadi a gasar Lig 1 ta Faransa, lamarin da ya sa aka cincibe shi akan gadon daukan mara lafiya cikin hawaye.
Sai dai kawo yanzu, PSG ba ta tabbatar da tsawon kwanakin da zai yi na jinya ba.

Kocin Real Madrid Zinedine Zidane ya yi fatan warkewar Neymar cikin hanzari don samun damar fafatawa da ‘yan wasansa da suka hada da Christiano Ronaldo.
PSG ta siyi dan wasan ne daga Barcelona akan farashin Pam miliyan 200 a cikin watan Agustan bara, in da ya ci ma ta kwallaye 29 cikin wasanni 30.

Copy the link below and Share with your Friends:

Download Our Official Android App on Google Playstore HERE
OR
Download from another source HERE



No comments:

Post a Comment